Obasanjo, Jonathan, Abdussalam, Gwamnoni Sun Hallara Don Taron Majalisar Magabata

Obasanjo, Jonathan, Abdussalam, Gwamnoni Sun Hallara Don Taron Majalisar Magabata

 • Rana ba ta karya, an shiga zaman jin shawaran magabata kan matsalolin da suka dabaibaye Najeriya
 • Majalisar magabata wata cibiya ce ta gwamnatin Najeriya wacce ke baiwa shugaban kasa shawara kan lamura masu muhimmanci
 • Lamarin Naira da tsadar mai sun tilasta shugaba Buhari son jin shawaran magabatansa

Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari a yau Jum'a ya shiga zaman majalisar magabata ta kasa domin tattaunawa da masu ruwa da tsaki kan matsalolin da suka dabaibaye Najeriya.

Matsalolin dake kan gaba yanzu sune sauya fasalin Naira da kuma tsadar man fetur.

Wadanda ke hallare a zaman sun hada da tsaffin shugabannin kasa Goodluck Jonathan; Yakubu Gowon, da Abdulsalami Abubakar, rahoton Channelstv.

Olusegun Obasanjo kuwa ya shiga ta yanar gizo.

Wadanda suka hallara a fadar shugaban kasa kuwa sune mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo; Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan; da Kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Muna Goyon Bayan Sauya Fasalin Naira Da Sharadi 1: Majalisar Magabata

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

council
Obasanjo, Jonathan, Abdussalam, Gwamnoni Sun Hallara Don Taron Majalisar Magabata Hoto: @BuhariSallau1
Asali: Twitter

Gwamnonin dake hallare da kafafunsu sune:

 1. Nasir El-Rufai (Kaduna)
 2. Darius Ishaku (Taraba),
 3. Babajide Sanwo-Olu (Lagos),
 4. Babagana Zulum (Borno).

Wadanda suka halarta ta yanar gizo sune:

 1. Ademola Adeleke (Osun),
 2. Abubakar Badaru (Jigawa), Yahaya Bello (Kogi),
 3. Atiku Bagudu (Kebbi), Dapo Abiodun (Ogun),
 4. Aminu Tambuwal (Sokoto),
 5. Simon Lalong (Plateau)
 6. Mataimakin gwamnan Nasarawa
 7. Mataimakin gwamnan Bauchi

Sauran wadanda ke wajen:

 1. Ministan birnin tarayya, Mohammed Bello;
 2. Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha;
 3. Antoni Janar kuma Ministan Shari'a Abubakar Malami
 4. Gwamnan bankin CBN Godwin Emefiele
 5. Shugaban hukumar INEC, Mahmoud Yakubu

Hafsun Sojin dake wajen:

 1. Shugaban hafsun tsaro, Janar Lucky Irabor
 2. Shugaban hafsun sojin kasa, Laftanan Janar Farouq Yahaya
 3. Shugaban hafsun sojin ruwa, Vice Admiral Awwal Gambo
 4. Shugaban hafsun sojin sama, AVM Ishiaka Amao

Kara karanta wannan

Gaskiya Ta Fito: Shugaba Buhari Ya Faɗa Wa Sarkin Musulmi Abu 3 da Suka Sa Ya Shiga Kamfen Tinubu

Sauran hukumomin tsaro:

 1. IGP na yan sanda, Baba Usman Alkali
 2. Kwamandan NSCDC, Dr Ahmed Abubakar Audi

Asali: Legit.ng

Online view pixel