Dama ta Samu: Matakai 5 na Mallakar Gida a Najeriya karkashin Shirin ‘Renewed Hope’

Dama ta Samu: Matakai 5 na Mallakar Gida a Najeriya karkashin Shirin ‘Renewed Hope’

  • Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta bullo da shirin samar da gidaje na Renewed Hope don magance matsalar karancin gidaje a Najeriya
  • Shirin samun gida na 'Renewed Hope', wanda ya shafi dukkan jihohi 36 da FCT, zai ba 'yan kasar damar saye kai tsaye da haya-zuwa-mallaka
  • Don mallakar wannan gida, dole ne mutane su ƙirƙiri asusu, duba nau'ikan gidajen, zaɓar tsarin da suka fi so, zaɓar hanyar biyan kuɗi, da sauransu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja — Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta kaddamar da sabon tsarin mallakar gidaje ga 'yan Najeriya na 'Renewed Hope.'

Wannan shiri dai ya zo ne a matsayin mayar da martani ga kalubalan gidaje da ‘yan Najeriya da dama ke fuskanta musamman a birane inda bukatar gidaje ta zarce wadata.

Kara karanta wannan

Hukumar kwastam ta bayyana abin da zai jawo a samu saukin farashin abinci

Bayani dalla dalla yadda za ka nemi gida a Najeriya karkashin shirin 'Renewed Hope.'
Matakan neman gida a Najeriya karkashin shirin 'Renewed Hope' na Tinubu
Asali: Getty Images

Wani hadimi ga shugaban kasa kan harkokin sadarwa na zamani, Daddy DO @DOlusegun, ya sanar da fara shirin ta shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake kira ga ‘yan Najeriya da su cike bukatar mallakar gidan, ya ce:

"Kada ku rasa damar zama masu gidan kansu a karkashin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta shirin mallakar gidajen 'Renewed Hope'.

Menene shirin mallakar gida na 'Renewed Hope'?

Shirin mallakar gida na 'Renewed Hope' shiri ne na gwamnatin Najeriya da nufin biyan bukatun gidaje a fadin kasar.

Wannan shirin ya shafi dukkan jihohi 36 da FCT, kuma gwamnatin tarayyar ta amince amince da gina gidaje 100,000 a duk fadin kasar a matsayin matakin farko.

Mutane masu kanana da matsakaitan samun kudi ne za su iya mallakar gidajen ta hanyar 'biya daya, zabin jinginar da kadara, ko kuma ta hanyar zaman haya zuwa mallaka.'

Kara karanta wannan

Zanga-zanga: Tinubu ya fadi yadda za a ci gajiyar shinkafar N40,000, ya saka ka'ida

Matakai 5 na mallakar gidan 'Renewed Hope'

1: Yi rajista: Domin samun damar siyan gidan kai tsaye ko ta hanyar jinginar da kadara, dole ne ku fara ƙirƙirar asusu a shafin shirin.

2. Nemo gidan: Yi amfani da akwatin bincike domin nemo gidan da ya dace da tsarin da kuke so (gari, wannan ya gina, farashi, nau'in, da sauransu).

3. Zaɓi gidan: Danna kan gidan da kake so domin ganin ƙarin bayanai. Ka duba hotunan gidan, abubuwan da ya kunsa da kuma yadda tsarin gininsa yake.

4. Zaɓi hanyar biyan kuɗi: Yanke shawarar ko siyan gidan a lokaci daya, ko neman jinginar kadara.

5. Biyan kudi: Biyan kuɗin da ake buƙata a cikin asusun da aka tanadar muku akan asusun da ka bude a shafin.

Wanene zai iya neman gidan?

Manya masu shekaru 18 zuwa sama waɗanda ke da tabbatacciyar hanyar samun kuɗi ko wurin aiki, kuma waɗanda ke ba da gudummawa ga asusun gidajen kasa, za su iya nema.

Kara karanta wannan

Zanga zangar adawa da 'mummunan mulki': 'Yan Najeriya sun yi martani ga jawabin Tinubu

Dole ne su kuma bi sharuɗɗa da ka'idojin siyarwa kuma su kammala cike bayan neman gidan a shafin shirin na yanar gizo.

"Mallakar gida na mun wahala" - Dangode

A wani labarin, mun ruwaito cewa attajirin da ya fi kowa kudi a Najeriya kuma na biyu a masu kudin Afrika, Aliko Dangote ya ce mallakar gida na masa wahala.

Dangote ya bayyana cewa bai mallaki gida ba a birnin Landan ko a ƙasae Amurka saboda baya son abin da zai ɗauke masa hankali inda ya ce ko a Abuja haya yake yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.