Bayan Caccakar Masu Zanga Zanga, Malamin Musulunci Ya Dawo kan ’Yan Kasuwa
- Sheikh Sani Umar Rijiyar Lemo ya dawo kan 'yan kasuwa da suke kara kudin kaya domin su ci kazamar riba a kasuwancinsu
- Shehin malamin ya gargade su da su ji tsron Allah saboda jefa al'umma cikin kunci da wasu daga cikinsu ke yi a yanzu
- Rijiyar Lemo ya ce babu dan kasuwa ko mai hali da zai samu albarka a dukiyarsa ba tare da tausayawa talakawa ba
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Sani Umar Rijiyar Lemo ya shawarci 'yan kasuwa kan kuntatawa mutane.
Shehin malamin ya ce babu albarka a kasuwancin dan kasuwa idan har bai saukakawa mutane ba yayin siye da siyarwa.
Rijiyar Lemo ya gargadi 'yan kasuwa
Malamin ya bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo da @el_uthmaan ya wallafa a shafinsa na X inda ya ja kunnensu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rijiyar Lemo ya ce idan har ubangiji ya cirewa attajira tausayi a zuciya to tabbas alama ce ta kasancewa cikin tsiya a lahira.
Sheikh Sani Umar ya ce abin takaici ne yadda ake kara kudin kaya saboda tashin dala amma kuma idan ta dawo baya babu rangwame.
Tsadar kaya: Rijiyar Lemo ya shawarci masu hali
"Yan kasuwarmu Musulmi su ji tsaoron Allah saboda ajiya ce da Ubagiji ya ba ku domin tashi a cikin salihan bayi a gobe kiyama'
"Mu tausayawa junanmu da kuma 'yan uwamnu kamar yadda Manzon Allah (SAW) ya yi umarni kan tausayin juna."
"Duk wani dan kasuwa da bai tausayawa talaka ba, ba zai kubuta a wurin Allah a gobe kiyama ba saboda zai iya rasa komai da yake da shi."
- Sheikh Rijiyar Lemo
Malamin ya ce duk wanda ba shi da tausayin al'umma a harkar kasuwancinsa a gobe kiyama zai tashi daga cikin fajirai.
Rijiyar Lemo ya caccaki masu zanga-zanga
A wani labarin, kun ji cewa Sheikh Sani Umar Rijiyar Lemo ya caccaki matasa kan shirin fita zanga-zanga a Najeriya.
Shehin malamin ya nuna damuwa kan yadda matasa ke yiwa malamai rashin kunya saboda suna kokarin hana su zanga-zangar.
Asali: Legit.ng