"Yadda Buhari, Kyari Suka Hana Ni Mallakar Rijiyoyin Mai ": Fitaccen Dan Kasuwa

"Yadda Buhari, Kyari Suka Hana Ni Mallakar Rijiyoyin Mai ": Fitaccen Dan Kasuwa

  • Hamshakin dan kasuwa a Najeriya, Tony Elumelu ya koka kan yadda aka dakile shi yayin da yake kokarin shiga harkokin mai a Najeriya
  • Elumelu ya ce tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari da marigayi Abba Kyari su suka hana shi samun damar mallakar rijiyoyin mai
  • Dan kasuwar ya ce an fada masa ba za a bar aiki mai muhimmanci irin wannan ga ya kasance a hannun kamfanoni ko mutane masu zaman kansu ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Fitaccen ɗan kasuwa a Najeriya, Tony Elumelu ya bayyana kalubale da ya fuskanta a harkar kasuwancinsa.

Elumelu ya fadi yadda tsohon shugaban kasa, Muhammad Buhari ya dakile mafarkinsa na mallakar rijiyoyin mai.

Kara karanta wannan

Bayan mayar da shi kotu, Ganduje ya fadi abin da za a yi wa bangaren shari'a

Dan kasuwar ya fadi yadda Buhari ya dakile masa mafarkinsa
Tony Elumelu ya zargi Muhammadu Buhari da hana shi mallakar matatar mai. Hoto: Pius Utomi Ekpei, Eric Piermont.
Asali: Getty Images

"Buhari ya hana ni mallakar rijiyar mai", Elumelu

Shugaban kamfanin mai na Heirs holdings oil and gas ya bayyana haka ne yayin hira da Financial Times a jiya Juma'a 9 ga watan Agustan 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Elumelu ya ce marigayi tsohon shugaban ma'aikatan Buhari, Abba Kyari shi ma ya taka rawa wurin dakile shirinsa na mallakar rijiyar man.

Dan kasuwar ya ce abin takaici ne duk da ware makudan kudi na daloli domin daukar nauyin shirin nasa, cewar This day.

Musabbabin hana Elumelu mallakar rijiyar mai

Fitaccen dan kasuwar ya ce an fada masa cewa Najeriya ba za ta bar irin wannan babban aiki a hannun kamfanoni masu zaman kansu ba.

Duk da haka, a shekarar 2021 Elumelu ya shiga harkar albarkatun mai gadan-gadan inda ya zuba makudan kudi a harkar.

Kara karanta wannan

Ana ƙoƙarin shawo kan Ndume, dan majalisa ya kara tsige gaskiya ga Tinubu

Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan Aliko Dangote ya zargi NNPCL da yi masa zangon-kasa a matatar mansa.

Dangote ya zargi NNPCL da zagon-kasa

A wani labarin, kun ji cewa fitaccen dan kasuwa a Afirka, Aliko Dangote ya bayyana kalubale da ya ke fuskanta kan matatar mansa.

Dangote ya ce akwai wasu ma'aikatan NNPCL da ke matatar mai a kasar Malta wadanda suke yi masa zangon-kasa.

Sai dai shugaban kamfanin ya musanta wannan zargi na Dangote inda ya ce babu kamshin gaskiya a ciki idan akwai haka kuma zai tabbatar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.