Machina: Gari a arewa da macizai ke da dangantaka mai kyau da mutane
Machina na daya daga cikin kauyuka koma baya a jihar Yobe. Kauyen na nan a kilomita 300 daga arewacin Damaturu, babban birnin jihar. Masarautar Machina tana da dumbin tarihi da al'adu dadaddu.
Daya daga cikin abin mamaki da garin mai tarihi ke da shi, shine yadda macizai da mutane ke mu'amala ba tare da sun cutar da juna ba.
Babu tabbacin lokacin da masarautar Machina ta fara abokantaka da macizai. Amma abu daya shine yadda jama'ar masarautar basu wasa da alakarsu da macizan.
Kiyayyar da ke tsakanin mutum da maciji za a iya cewa tun bayan halittarsu ne, amma jama'ar Machina basu cutar da macizai kwata-kwata.
A fadar mai martaba sarkin Machina, Alhaji Bashir Albishir Bukar Machinama, OON, yayi bayanin dangantakar da ke tsakanin macizan da kuma illar cutar dasu.
Ya ce: "Dangantaka tsakanin jama'a da kuma macizan garin nan tana daga cikin abubuwan da mutane ke son sani a Machina. Hakan na da dumbin tarihi.
"Iyayenmu na fada mana cewa kada mu kashe macizai saboda a fadar nan, akwai lokacin da matar sarki ta haifa mutum da maciji. Macijin yayi kwanaki a kalla uku a fadar nan.
"Saboda ba zai iya rayuwa a cikin jama'a ba, sai ya shige cikin duwatsu. Kun san fadar tana kusa da tsaunika ne. Yakamata mutane su sani cewa ba ni, mahaifina ko kakana bane aka haifa tare da maciji, daya daga cikin shugabannin Machina ne.
KU KARANTA: Bayan korata a wajen aiki iyalina ta gudu, yanzu kuma tana so ta dawo bayan taji na sami miliyan 15 - Wani na neman shawara
"Idan muna farin ciki, kowanne iri kuwa a fada, muna ganin macizai na fitowa. Idan wani abin alheri ko na sharri zai faru damu, za ka ga macizai na fitowa. Kawai dai muna ganinsu, mu kan yi fatan alheri ne. Mutane da yawa basu ganinsu amma idan mutum yayi sa'a, ya kan gansu suna yawo a fadar.
"Akwai inda nake hutawa da yamma, macizai na zuwa kasan kujerata su zauna na wani lokaci sannan su wuce. Basu cutar da kowa. Yawonsu kadai suke yi sannan su wuce. Saboda haka ne muke daukar macizan a matsayin 'yan uwanmu na jini, don haka ne bamu kashesu a Machina."yace.
Da aka tambaya sarkin ko akwai abinda wanda ya kashe maciji a garin yake fuskanta, sai sarkin yace: "Tabbas na san akwai abinda duk wanda ya kashe maciji ke fuskanta. Akwai wani matashi da yaje gona da mahaifina suna gyara. Sai ya ga wani maciji, tuni kuwa ya dau sanda ya kashe shi. Babu dadewa ya fadi aka daukeshi sai gida. Dare nayi macizan suka dinga shiga gidanshi don ko bacci ya kasa. Tuni jikin shi yayi laushi ya fara tafiyar macizan tare da komawa yanayinsu. Bayan an sanar da sarkin ne ya bashi magunguna sannan aka roki macizan su yafe mishi. Sai da ya dau kwanaki a fada sannan ya warware ya koma gidan shi."
Ya kara da cewa, "Amma kuma, duk idan shekara ta zagayo, sai matashin ya fada irin rashin lafiyar kuma sai ya sha maganin yake komawa daidai. Sai da ya dau shekaru 40 a haka har bayan rasuwar mahaifina. Ni na ci gaba da bada wannan maganin har zuwa mutuwar shi a shekaru uku da suka gabata. Wannan ne illar kashe macizai."
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng