Wasu Sun Nemi a Cafke ‘Dan Bello, Yaron El Rufai Ya ba Mai Barkwanci Shawarar Ya Yi Hattara

Wasu Sun Nemi a Cafke ‘Dan Bello, Yaron El Rufai Ya ba Mai Barkwanci Shawarar Ya Yi Hattara

  • Bashir El-Rufai yana cikin masu bibiyar bidiyoyin Bello Habib Galadanci wanda yanzu ya shahara a dandalin sada zumunta
  • Yaron tsohon gwamnan na jihar Kaduna ya ba Dan Bello shawarar ya yi hattara, ya guji yin abin da zai jefa shi a matsala
  • Daga cikin shawarwarin da Malam Bashir El-Rufai ya ba da shi ne mai wasan ya guji bata sunan shugaban kasa babu dalili

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Yayin da tauraruwarsa ta ke haskawa, Bashir El-Rufai ya yi kira ga Bello Habib Galadanci wanda aka fi sani da Dan Bello.

Malam Bashir El-Rufai ya fadawa Bello Habib Galadanci ya yi hattara da yadda yake fitar da bidiyoyi da kokarin fadakar da al’umma.

Kara karanta wannan

Farfesa ya fallasa dabarar turawa wajen shigowa Najeriya da akidun LGBTQ a boye

Dan Bello
Dan Bello ya na sukar shugabanni a bidiyoyinsa Hoto: Aliyu Jalal/Olusegun Dada
Asali: Facebook

Shawarar Bashir El-Rufai ga Dan Bello

Malam Bashir El-Rufai ya yi magana a shafinsa na X inda yake cewa ya kamata tsohon ‘dan jaridan ya yi hattara da irin bidiyon da yake yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ina cikin masoya Dan Bello, amma ina tunanin ya kamata ya yi a hankali fa!"

- Bashir El-Rufai

Dan Bello zai taba El-Rufai

Da wasu su ka ankarar da shi cewa nan gaba zai iya yin bidiyo a kan mahaifinsa, Nasir El-Rufai, sai ya nuna hakan ba matsala ba ne.

Bashir yake cewa Galadanci ya taba yin bidiyo a kan tsohon gwamnan kuma har ya nuna masa, su ka yi ta dariya ya burge El-Rufai.

...Dan Bello ya matsawa gwamnati

Bisa dukkan alamu, malamin makarantar kuma mai yin bidiyon fadakarwa cikin barkwanci ya taso gwamnatin Bola Ahmad Tinubu a gaba.

Kara karanta wannan

"Yadda Buhari, Kyari suka hana ni mallakar rijiyoyin mai ": Fitaccen dan kasuwa

A ‘yan kwanakin nan Bello Galadanci wanda ya fi shahara da ‘Dan Bello a dandalin sada zumunta da nufin fallasa gwamnatin tarayya.

Dan Bello ya yi bidiyo inda ya yi zargin akwai mummunar badakala wajen shigo da tattacen mai daga kasar Malta wanda ya jawo surutu.

Ko Dan Bello zai karbi shawara?

Daga baya Bashir El-Rufai ya kara da yin gargadi a kan fitar da bidiyon da ke zargin shugaban kasa da laifi ba tare da wasu hujjoji ba.

A ra’ayin Bashir bai kamata a rika yin duk abin da zai iya bata sunan shugaban kasa ba musamman da aka yi wa Najeriya bakin tabo.

Nasarorin gwamnatin Tinubu a shekara 1

A baya kun samu labari cewa duk da mafi yawan jama’a su na kuka da tsadar rayuwa, akwai wasu nasarorin da aka samu a mulkin APC.

A yayin da Bola Tinubu ya hau karagar mulki, N30, 000 ne mafi karancin albashin talaka, amma yanzu gwamnati ta maida shi N70, 000.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng