Ned Nwoko: Fitaccen Sanatan PDP Ya Mutu a Kasar Switzerland? Gaskiya Ta Fito

Ned Nwoko: Fitaccen Sanatan PDP Ya Mutu a Kasar Switzerland? Gaskiya Ta Fito

  • Ned Nwoko ya yi watsi da rahotannin da ke cewa ya rasu a kasar Switzerland yana mai cewa jita-jita ce kawai ake yadawa
  • Nwoko mai wakiltar Delta ta Arewa a wata sanarwa a ranar Juma’a a Abuja, ya ce rahotannin gaba daya karya ne tsagoronta
  • 'Dan majalisar ya nuna takaici kan yadda ake kokarin bata masa suna da ci masa zarafi bayan ya ba wata 'yar yarinya kyautar mota

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Fitaccen sanatan Najeriya daga jihar Delta, Sanata Ned Nwoko ya yi magana yayin da jita-jita ta karade intanet cewa ya rasu.

Sanata Nwoko daga jam'iyyar PDP ya fara kokawa da yadda 'yan soshiyal midiya ke yawan yin rubuce rubucen karya da cin zarafi a kansa.

Kara karanta wannan

Gwamna ya fadi babban darasin da gwamnonin Arewa suka dauka daga zanga zangar yunwa

Sanata Ned Nwoko da aka ce ya mutu ya yi magana
Sanata Ned Nwoko ya karyata masu yada rahoton cewa ya mutu. Hoto: Officialprincened
Asali: Facebook

Sanata Ned Nwoko yana nan da ransa

Jaridar The Punch ta ruwaito sanatan wanda ke wakiltar mazabar Delta ta Arewa ya fitar da sanarwa a ranar Juma'a a Abuja inda ya ce labarin 'karya' ake yadawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dan majalisar dattawan ya ce yana nan da ransa sabanin yadda wasu ko buga rahoton cewa ya mutu a kasar Switzerland.

A cewar sanatan:

"Wadannan rahotannin ba gaskiya ba ne. Karya ce kawai aka shirya domin cimma wata manufa. Hakika hakuri na ya kare kan masu yada jita-jitar karya a kaina."

Sanata Nwoko zai dauki matakin shari'a

Sanata Ned Nwoko ya nuna takaici kan yadda ake kokarin bata masa suna da ci masa zarafi in ji rahoton jaridar Tribune.

Dan majalisar dattawan ya ce:

"A cikin 'yan makonnin nan, an samu wasu bata gari suna cin mutunci da zagina saboda na sayawa wata yarinya mai wasan barkwanci mota.

Kara karanta wannan

Ribar zanga zanga: An fara maganar yunkurin inganta rayuwa a Arewa

"Zan dauki matakin shari'a na gaggawa kan masu yada karairayi ko cin zarafina. Lallai za a kama masu laifin kuma za su girbi abin da suka shuka.

Sanata Nwoko ya yi gargadin cewa ba zai lamunci ci gaba da bata masa suna ba kuma ba zai kara nuna sassauci kan masu aikata hakan ba.

Matsalar tsaro: Sanata ya gabatar da kuduri

A wani labarin, mun ruwaito cewa sanata mai wakiltar mazabar Delta ta Arewa, Ned Nwoko, ya yi magana game da ba ‘yan Najeriya damar mallakar bindiga saboda tabarbarewar tsaro.

Sanata Nwoko ya bayyana cewa kudirin da ya gabatar na 'kare kai da ka’idojin mallakar bindigogi' zai ba wadanda suka cancata damar mallakar bindiga ne kawai.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.