Tinubu Zai Fitar da N280bn: An Shirya Karasa Gina Kilomita 82 na Babban Titin Arewa

Tinubu Zai Fitar da N280bn: An Shirya Karasa Gina Kilomita 82 na Babban Titin Arewa

  • Gwamnatin tarayya ta sanar da shirinta na karasa bangaren da kamfanin Julius Berger yake yi na ginin babbar hanyar Abuja zuwa Kano
  • Ministan ayyuka, David Umahi ya ce gwamnati za ta rika biyan Julius Berger Naira biliyan 20 duk wata har zuwa lokacin kammala gina titin
  • A cewar ministan, an ware Naira biliyan 280 domin kammala gina titin a cikin watanni 14 yayin da ya bayyana dalilin tsaikon da aka samu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta shirya karasa gina babbar hanyar Arewa wadda ta taso daga Abuja zuwa Kano a cikinn watanni 14.

Ministan ayyuka, Sanata David Umahi ya ce gwamnatin tarayya za ta rika biyan kamfanin Julius Berger Naira biliyan 20 kowanne wata na tsawon watanni 14.

Kara karanta wannan

Ya gama sukar Tinubu, matsala 1 ta taso Gwamnan PDP ya nemi agajin Shugaban kasa

Gwamnatin tarayya ta yi magana kan karasa titin Abuja zuwa Kano
Gwamnatin Najeriya za ta biya Julius Berger N280bn domin karasa titin Abuja zuwa Kano. Hoto: @PBATMediaCentre
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa jimillar kudin za ta kama Naira biliyan 280 inda ake sa ran Julius Berger ya kammala bangaren da ya fara ginawa a shekara biyu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnati na kukan rashin kudin gina titi

Ministan a wani taro da kamfanin domin duba kwangilar gina titin, ya koka kan karancin kudi da gwamnati ke fama da shi wanda ya jawo tsaiko wajen kammala aikin.

Ministan ya ce a halin yanzu gwamnatin tarayya na kokarin kammala gina titunan Abuja-Kaduna-Zariya-Kano da kashi na biyu na hanyar Legas-Ibadan.

Sauran titunan sun hada da gadar Neja ta biyu, gadar Mainland ta uku, gadar Iddo da kuma gadar Carter, wadanda ya ce dukkaninsu suna da matukar muhimmanci.

Gwamnati ta yi matsaya kan titin Abuja-Kano

Sanarwar ta kara da cewa:

“Bisa umarnin majalisar zartaswa ta tarayya dangane da karasa ayyukan da aka gada da wadanda aka fara, ma’aikatar ayyuka ta tarayya ta yi matsaya da Julius Berger.

Kara karanta wannan

Minista ya tona asirin gwamnoni, ya faɗi gwamna da ke sauya shinkafar tallafin Tinubu

“A bangaren titin Abuja-Kaduna-Zaria-Kano, gwamnati ta amincewa Julius Berger ya karasa bangaren da yake yi tare da yabawa kamfanin saboda ingancin aikin da yake yi.
"Ministan ya amince cewa aikin bangarensu zai dauki tsawon watanni 14. Kuma za a yi aikin a matakai hudu, yayin da gwamnati za ta rika biyan N20bn duk wata har a kammala aikin."

Titin Abuja-Kano zai ci N1.35tr

A wani labarin mun ruwaito cewa ministan ayyuka, David Umahi ya ce aikin gina titin Abuja zuwa Kano ya tashi daga N165bn ya koma N1.35tr.

Sanata David Umahi ya ce kamfanin Julius Berger, ya fadi masu cewa sashen aikin na hanyar Abuja-Kano zai ci N1.35tr sabanin yadda cinikin ya kaya da gwamnatin Muhammadu Buhari.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.