Doguwa v Jibrin: 'Dan Majalisar APC Ya Karyata Zargin Kashe Rayuka a Kano domin Cin Zabe

Doguwa v Jibrin: 'Dan Majalisar APC Ya Karyata Zargin Kashe Rayuka a Kano domin Cin Zabe

  • Ce-ce-ku-ce ya barke a tsakanin wakilan mutanen Kano, Alhassan Ado Doguwa da AbdulMumin Jibrin Kofa bisa zargin kashe 'yan adawa
  • Dan majalisa, AbdulMumin Jibrin Kofa ne ya yi ikirarin Doguwa ya na amfani da karfi da gumin jama'ar yankinsa wajen murde zabuka a yankin
  • Amma Hon Doguwa ya bugi kirji inda ya musanta zargin Hon Kofa, tare da bukatar ya bayar da shaidar da ke nuna shi ya yi kisan kan ko karfa karfa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Jihar Kano - Dan majalisa mai wakiltar Tudun Wada da Doguwa ya fusata bisa yadda takwaransa mai wakiltar Kiru da Bebeji, AbdulMumin Jibrin Kofa ya zarge shi da kisan kai.

Hon . Jibin Kofa wanda shi ne shugaban kwamitin gidaje a majalisar wakilai ya yi zargin Hon. Doguwa da kashe 'yan adawa bakwai yayin gangamin neman zabe.

Kara karanta wannan

Betta Edu za ta koma kujerar minista? Tinubu ya yi muhimman sauye sauye a ma'aikatar jin ƙai

Doguwa
Hon. Alhassan Ado Doguwa ya musanta kashe 'yan adawa a 2019 Hoto: Alhassan Ado Doguwa TV/@AbdulAbmJ
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa a martaninsa, Hon. Ado Alasan Doguwa ya kalubalanci Hon. Kofa da ya nuna hujjar da ke nuna ya kashe mutane lokacin zabe.

'Dan majalisar na NNPP ya yi ikirarin sai da aka rasa rayuka domin Doguwa ya lashe zabe a APC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai Doguwa ya ce ko a baya, kotu ta wanke shi daga zargin kisan kai tare da umartar gwamantin Kano ta biya shi N25m na bata masa suna da lokaci.

"Ku yi watsi da sharrin Kofa," Doguwa

Shugaban kwamitin fetur a majalisar wakilai, Hon. Ado Doguwa ya ba wa dattijan jam'iyya da sauran abokansa hakuri bisa zarginsa da kisan kai da aka yi a wani kokari ma bata masa suna.

Hon. Doguwa ya bayyana cewa wakilan NNPP na rura wutar rikici tsakaninsa da jama'ar da ya ke wakilta, bayan sharri ne da bita da kulli kawai irin na siyasa, Daily Nigerian ta wallafa.

Kara karanta wannan

"Manyan Arewa da za su iya rarrashin masu zanga zanga," masoyin Tinubu ya fadi sunaye 2

Ado Doguwa ya ce har yanzu ya na jiran ikirarin da ɗan majalisa Kofa ya yi na cewa zai fallasa abin da zai sa jam'iyyar APC ta kore shi daga cikinta.

Ado Doguwa ya caccaki Jibrin Kofa

A baya kun ji dan majalisar wakilai mai wakiltar Tudun Wada da Doguwa, Hon. Alhassan Ado Doguwa ya caccaki takwaransa da Kiru da Bebeji, AbdulMumin Jibrin Kofa.

Wannan ya biyo bayan zargin da Hon. Kofa ya yi masa na cin mutuncin jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabi'u Kwankwaso wanda Doguwa ya ce ya na mutuntawa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.