Kai Tsaye: Yadda Zanga Zanga Ke Gudana a Manyan Biranen Arewacin Najeriya

Kai Tsaye: Yadda Zanga Zanga Ke Gudana a Manyan Biranen Arewacin Najeriya

A yau Alhamis 1 ga watan Agustan 2024 aka fara gudanar da zanga-zanga a fadin Najeriya baki daya.

Za mu kawo muku rahotanni kan yadda abubuwa ke tafiya a halin yanzu musamman a manyan biranen Arewacin Najeriya.

Idan baku manta ba, 'yan Najeriya sun yi alkawarin fita zanga-zanga ne bayan da yunwa da fatara ta yi masu katutu tun bayan hawan shugaba Tinubu mulki.

Sun yi korafin cewa, gwamnatin Tinubu ta gaza sauraran kokensu tare da biya masu bukatu, sai dai ma ta kara tunzura su tare da yi masu kallon shawaraki.

Yau dai ta tabbata, an fito zanga-zangar da ake kyautata zaton za a yi kwanaki akalla goma ana yi.

Fatanmu, a yi lafiya, a kammala lafiya kuma a samu sulhu tsakanin gwamnatin Najeriya da 'yan kasar.

An sanya dokar hana fita a Nasarawa

Shugaban karamar hukumar Karu, James Thomas, ya sanya dokar hana fita a fadin Karu daga karfe 6 na yamma zuwa 6 na safe daga yau har zuwa wani lokaci.

Karu, karamar hukuma ce da ke a jihar Nasarawa wadda kume ke makotaka da babban birnin tarayya Abuja, inda aka samu rahoton bullar tashin hankula.

Channels TV ta ruwaito cewa mai taimakawa shugaban karamar hukumar Karu ta fuskar yada labarai Danbaba Magaji ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis.

An kashe mutane 17 a zanga-zangar yunwa

Jaridar The Punch ta ce akalla mutane 17 ne ake fargabar an kashe a Abuja, Kano, Neja, Borno, Kaduna da Jigawa yayin zanga-zangar yunwa da aka gudanar a jiya Alhamis.

An harbe mutum daya a Abuja da Kano, biyu aka kashe a Jigawa, an ce jami’an tsaro sun harbe wasu shida a Neja, yayin da hudu suka mutu a Borno, uku kuma a Kaduna.

An sanya dokar ta baci a Katsina

Mukaddashin gwamnan jihar Katsina, Farouq Lawal Jobe ya sanar da sanya dokar hana fita ta awanni 24 a karamar hukumar Dustinma.

A sauran kananan hukumomin jihar kuwa, dokar hana fitar za ta yi aiki daga karfe 7 na yamma zuwa karfe 7 na safe, inji rahoton Channels.

Mukaddashin gwamnan ya ce ya dauki wannan mataki domin kare rayuwakan al'umma da kuma wanzar da zaman lafiya.

Masu zanga-zanga sun isa gidan Buhari a Daura

Mutane da suka fito zanga-zanga a garin Daura, sun yi dafifi a kusa da gidan tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.

'Yan sanda sun ba masu zanga-zanga kariya a Bauchi

Jami'an 'yan sanda sun ba masu zanga-zangar adawa da halin ƙunci da tsadar rayuwa kariya a Bauchi.

'Yan sanda sun yi himma, an cafke masu fasa shaguna a Kano

Rundunar 'yan sandan Kano ta cafke wasu matasa da ake zargin sun fasa shaguna tare da kwashe jarkokin mai da sunan ganima yayin zanga-zanga.

A sakon da Kakakin rundunar'yan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna ya wallafa a shafinsa na Facebook, an gano matasan ciki har da yara masu kananan shekaru da kayan 'ganima'.

"Wannan abin da ake yi ba zanga-zanga ba ne, ya koma satar kayan mutane."

-SP Abdullahi Haruna Kiyawa

Matasa sun fara balle shaguna mutane a Kano

Rahotanni da muke samu sun tabbatar da cewa matasa sun balle shagunan mutane yayin zanga-zanga a Kano.

BBC Hausa ta wallafa wani bidiyo da matasan ke dibar kaya a shaguna bayan sun balle su a birnin.

Sai dai kuma a gefe guda akwai wasu matasan da ke gudanar da zanga-zangar lumana ba tare da tashin hankali ba.

Matasa sun afkawa gidan man NNPCL a Kano

Matasa a Kano sun afkawa gidan man fetur na NNPCL a Kano tare da fasa wasu kayayyakin da ke harabar gidan man.

Bata-garin sun balle akalla kawunan mai guda 10 a gidan man da ke Hotoro ring road wuraren Eastern Bye-pass.

Haka kuma an lalata gilasai motar dakon mai guda uku, tare da sace wasu kayayyakin da ke cikin motar.

Wani da lamarin ke faruwa a kan idonsa, Saddam Musa ya shaidawa Legit cewa lamarin na kokarin ya fi karfin jami'an tsaro.

An gwabza tsakanin jami'an tsaro da masu zanga-zanga

Jami'an tsaro suna cigaba da gwabzawa da masu zanga-zanga a Gwagwalada da ke birnin Abuja.

Masu zanga-zangar sun tare hanyar Lokoja zuwa Abuja wanda hakan ya dakile zirga-zirgan ababawan hawa.

Daily Trust ta tattaro cewa an farfasa ababawan hawa da dama inda lamarin ya kamari kamari.

Ana kokarin fasa shagon Garba Karfe

Jami’an ‘yan sanda sun dage sun hana bata-gari aukawa babban shagon Garba karfe da ke unguwar Na’ibawa a jihar Kano.

Dakarun ‘yan sanda sun bukaci masu zanga-zanga sun koma tsallaken titi domin gudun a fasa shagon, a saci dinbin dukiyoyi.

An soma barna kafin fara zanga-zanga

Tun cikin daren yau Legit ta samu labari an fasa shagon Rufaidah da ke Hotoro a Tarauni.

Daga baya an samu labarin fusatattun matasa da bata-gari fasa wani shagon na Rufaidah inda ake saida madara a yankin Rijiyar Lemu.

Zanga-zanga a Gombe

A Gombe, masu zanga-zanga sun cika gari sun hau titi har zuwa gidan gwamnati inda aka ji su na kiran sunan shugaban kasa da Inuwa Yahaya.

Dazu da karfe 11:00 na safe, wata mazauniyar garin Gombe, ta tabbatar mana cewa su na jin jami’an tsaro su na koro mutane da borkonon tsohuwa.

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.