Mata Ta Shiga Hannun 'Yan Sanda, Ana Zargin ta Kashe Mijinta da Duka, Ta Birne Shi a Abuja

Mata Ta Shiga Hannun 'Yan Sanda, Ana Zargin ta Kashe Mijinta da Duka, Ta Birne Shi a Abuja

  • Wata mata ‘yar shekara 23 mai suna Rahimat Salaum ta shiga hannun 'yan sanda bayan zargin kashe mijinta, Shehu Salaum
  • Tana kokarin guduwa da kayan mijin nata lokacin da aka kama ta kamar yadda sanarwar rundunar 'yan sandan Abuja ta nuna
  • Sanarwar ta ce wanda ake zargin ta amsa laifin kashe mijin nata tare da kai jami'an 'yan sanda inda ta binne gawar bayan ta konata

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Ana zargin Rahimat Salaum, wata matar aure mai shekara 23 da laifin kashe mijinta mai suna Shehu a wata rigima da ta kaure tsakaninsu a babban birnin tarayya.

An ruwaito cewa jami’an ‘yan sandan Abuja da ke aiki da sashin ‘yan sanda na Pegi ne suka cafke matar a lokacin da take shirin guduwa da kayan mijinta.

Kara karanta wannan

Tana gama rera waka, fitacciyar jarumar Nollywood ta yanke jiki ta fadi matacciya

'Yan sanda sun kama matar aure da laifin kashe mijinta tare da kone gawarsa
Matar aure ta amsa laifin kashe mijinta tare da kokarin guduwa da kayansa a Abuja. Hoto: @Jossy_Dannyking
Asali: Twitter

Matar aure ta kashe mijinta a Abuja

Jami’ar hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan FCT, Josephine Adeh ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar a shafinta na X a ranar Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Josephine Adeh ta ce wadda ake zargin ta yi yunkurin guduwa da kayan mijin nata mai shanyewar jiki a cikin karamar mota lokacin da ‘yan sanda suka kutsa kai gidan suka kama ta.

Sanarwar ta kara da cewa, bayan da aka yi mata tambayoyi, wanda ake zargin ta amince da kashe mijinta bayan fadan da ya barke a tsakaninsu.

An gano gawar mijin da aka kashe

Rundunar ‘yan sandan ta ce daga bisani wadda ake zargin ta kai jami’anta zuwa wani gini da ba a kammala ba inda ta jefar da gawar mijin bayan ta babbake ta.

Kara karanta wannan

Kasa da kwana 2 a fara zanga zanga, hukumar kashe gobara ta aika sako ga 'yan Najeriya

Sanarwar ta ci gaba da cewa, yayin da aka fara bincike, kwamishinan ‘yan sanda na babban birnin tarayya Abuja, CP Benneth Igweh, ya tabbatar da cewa za a yi adalci kan lamarin.

Ya kuma bukaci mazauna yankin da su kara sanya ido kan abubuwan da ke faruwa a yankunansu kuma su kai rahoton duk wani abu da basu gamsu da shi ba ga hukumomin tsaro.

Amarya ta halaka mijinta a Neja

A wani labarin, mun ruwaito cewa wata sabuwar amarya yar shekara 20 mai suna Aisha Aliyu da ke a karamar hukumar Lapai a jihar Neja ta kashe mijinta, Idris Ahmadu.

An ce amaryar wacce ba ta cika wata biyu ba a dakin mijinta ta yanke shawarar salwantar da ransa ta hanyar daba masa wuka yayin da rundunar 'yan sanda ke ci gaba da bincike.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.