Yanzu-yanzu: Kotu ta kama Maryam Sanda da laifin kashe mijinta
Wata kotu birnin tarayya dake unguwar Maitama ta kaddamar da zama kan shari'ar Maryam Sanda, da ake tuhuma da laifin kisan kai kuma kotu ta tabbatar da zargin, ita ta kashe mijinta.
Ana gurfanar da ita ne kan zargin kashe mijinta, Bilyaminu Bello, wanda yake dan'uwan tsohon shugaban PDP, Alhaji Bello Halliru Muhammad a 2017.
An gurfanar da ita tare da dan 'uwanta, Aliyu Sanda; mahaifiyarta, Maimuna Aliyu, da mai aikin gidanta, Sadiya Aminu, wadanda ake tuhuma da kokarin boye gaskiya ta hanyar goge jinin marigayin bayan kisansa.
Bayan kammala muhawara tsakanin lauyoyi da rubuta hujjojin dukkan bangarorin biyu ranar 25 ga Nuwamba, 2019, Alkali mai shari'a, Jastis Yusuf Halilu, ya zabi yau 27 ga Junairu, domin yanke hukunci.
KU KARANTA: Yanzu-yanzu: EFCC ta gurfanar da Shehu Sani a kotu
A ranar Laraba, 3 ga watan Yuli, 2018, kotu ta bada belin Maryam Sanda wacce ke garkame a kurkuku da laifin kisan mijinta.
Jastis Yusuf Halilu wanda ya ki bada beli a baya ya bayyana cewa akwai wani dalili kwakkwara da ya gamsar da shi kuma ya sa ya bada belin.
Alkalin ya ce rahoton asibiti ya nuna cewa Maryam na cikin wani mugun hali da jami’an fursunonin ba zasu iya kula da ita ba kuma ya gamsu ne saboda banda cewa tanada juna biyu, tana fama da ciwon Asthma.
Kwana daya kacal bayan babban kotun da ke Abuja ta bayar da belin Maryam Sanda, wadda ake tuhuma da laifin kashe mijinta ta hanyar daba masa wuka har lahira ta shirya wa yar ta party na murnar zagayowar ranar haihuwa.
Marigayi mijin nata dan uwa ne ga tsohon shugaban jam'iyyar PDP, Halliru Bello.
Taron murnar zagayowar haihuwar dai anyi shi ne ranar Alhamis, 8 ga watan Fabrairu a gidan mahaifiyar Maryam kuma ya samu hallartan yan uwan ta na jiki.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng