An saki Matar da ta kashe mijinta a Kano bayan shekaru 7 a Kurkuku

An saki Matar da ta kashe mijinta a Kano bayan shekaru 7 a Kurkuku

  • Bayan shekaru bakwai da tsareta, an yafewa Rahama Hussaini da ta kashe mijinta
  • Gwamnati ta saketa ne bisa shawarar da kwamitin rage cinkoso cikin gidajen yari ta bada
  • Rahma ta kashe mijinta tana yar shekara 16 bayan kasa da mako guda da aure

Kano - Kwamitin gyara da rage yawan mutane a gidajen yari ta saki Rahma Husseini, budurwar da kotu ta kama da laifin kashe mijinta a jihar Kano shekaru bakwai da suka gabata.

Kwamitin karkashin jagorancin Alkali Ishaq Bello, ta taimaka wajen sakin wasu fursunoni 30 daga gidajen yari daban-daban a ranar Juma'a, rahoton DailyNigerian.

Zaku tuna cewa a 2014, an damke Rahma Hussein, da laifin kashe mijinta rana daya bayan daurin aurensu.

Alkali R.A Sadik a 2018 ya bada umurnin jefa ta kurkuku amma zuwa lokacin da gwamnan jihar yaga dama saboda an yi mata auren dole ne kuma an yi mata aure tana yar shekara 16.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Zamfara ta ba da umarnin rufe kasuwanni da tashoshin man fetur, ta bayyana dalili

Tun daga lokacin, babu gwamnan da ya waiwayi lamarin sai yanzu da kwamitin ta kai ziyara gidajen yari don rage yawan fursunoni.

Kakakin gidajen yarin Kano, Musbahu Kofar-Nassarawa, yace an saketa ne bisa shawarar jami'an gidan yarin saboda tana da halayya na kwarai.

A cewarsa, kwamitin ta baiwa gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje, shawara ya duba lamarin a yafe mata tun da Alkali ya jingine hukuncinta ne da ganin daman gwamna.

Yace gwamnan ya karbi shawarar kuma ya yafe mata.

Bayan saketa, Rahma Hussein, cikin farin ciki ta godewa kwamitin, gwamna Ganduje, da jami'an gidan yarin da suka taimaka wajen sakinta.

Rahama cikin hawaye tace:

"Ina godiya ga wannan kwamitin, Allah ya saka muku. Jami'an Kurkukun da suka bada shawaran sakeni, Allah ya saka muku."

Kara karanta wannan

Rufe Makarantun Kaduna: Iyayen Ɗalibai Sun Ce Sun Fara Tura Ƴaƴansu Koyon Ɗinki Da Walda

An saki budurwar da ta kashe mijinta a Kano bayan shekaru 7 a Kurkuku
An saki budurwar da ta kashe mijinta a Kano bayan shekaru 7 a Kurkuku Hoto: Daily Nigerian
Asali: Facebook

Waiwaye kan abinda Rahma tayi

A 2014, an zargi Rahma Hussein da laifin kashe mijinta, Tijjani Basiru, a unguwar Darmanawa dake karamar hukumar Tarauni, kasa da mako daya bayan aurensu.

Da farko da aka gurfanar da ita a kotu ta karyata zargin. Amma bayan shekaru uku, ta amince da cewa lallai ta aikata laifin lokacin da take shekaru 16.

Alkali RA Sadiq yayin yanke hukunci, yace dokar Penal Code tace kotu ba zata ita iya yanke hukuncin kisa kan mai ciki da mutum mai kasa da shekaru 17 ba.

Sai Alkali ya bada umurnin jefa ta kurkuku amma zuwa lokacin da gwamnan jihar yaga dama saboda an yi mata auren dole ne kuma an yi mata aure tana yar shekara 16.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng