Zance ya kare: Lauya ta kashe mijinta, ta cire gabansa ta cinye gaba daya

Zance ya kare: Lauya ta kashe mijinta, ta cire gabansa ta cinye gaba daya

- Gwamnatin jihar Legas ta gurfanar da wata mata mai suna Mrs Udeme a kan laifin kashe mijinta tare da tsinke mazakutar shi

- Wadannan laifukan kuwa abin hukuntawa ne a sashi na 165 da 223 na dokokin laifukan jihar Legas na 2015

- Wannan ne lauya na biyu da lauya mace ta taba kashewa a jihar bayan zarginsu da cin amana da lauyoyin matansu suka yi

Gwamnatin jihar Legas ta gurfanar da wata mata mai suna Mrs Udeme mai shekaru 47 a kan zargin kisan kai da kuma tozarta gawa.

Duk da matar ta musanta zargin da ake mata, dan sanda mai shigar da kara, Sunmonu Babatunde, ya sanar da kotun cewa wacce ake zargin ta aikata abinda ake zargin ta da shi ne a ranar 3 ga watan Mayu a rukunin gidaje na Diamond, Sanotedo dake Lekki a jihar Legas.

Zance ya kare: Lauya ta kashe mijinta, ta cire gabansa ta cinye gaba daya
Zance ya kare: Lauya ta kashe mijinta, ta cire gabansa ta cinye gaba daya
Asali: Facebook

Ya ce wacce ake zargin ta soki mijinta da wuka kuma ta lalata gawar shi ta hanyar yanke mazakutar shi.

Wannan laifin ya ci karo da tanadin sashi na 165 da sashi na 223 na dokokin laifuka na jihar Legas na 2015.

Sashi na 165 ya tanadar da shekaru 5 a gidan gyaran hali inda sashi na 223 ya tanadar da hukuncin kisa.

KU KARANTA: Wata sabuwa: Matan Najeriya sun zo na 15 a jerin matan da suka fi iskanci a duniya a kasashen duniya

Alkali Adedayo Akintoye ya bukaci a adana wacce ake zargin a gidan gyaran hali kuma ya dage sauraron shari'ar zuwa ranar 8 da 9 ga watan Oktoba, kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito cewa wacce ake zargin ta fara gurfana ne a gaban wata kotun Majistare da ke Yaba amma an garkameta a gidan gyaran hali kafin a samu shawara kan shari'ar daga daraktan gurfanarwa na jihar.

Syphorosa Otike- Odibi, lauyan da aka kashe dan asalin jihar Delta shi ne mutum na biyu da lauya mace ta kashe.

Lauya ta farko da ta fara aikata irin laifin ita ce Yewande Oyediran mai aiki da ma'aikatar shari'a ta jihar Oyo.

Yewande ta soki mijinta mai suna Lowo Oyedidan Ajanaku mai shekaru 38 a rukunin gidaje na Akobo da ke Ibadan, jihar Oyo a ranar 2 ga watan Fabrairu, 2016. Hakan ya faru ne bayan da ta gane yana da wani da tare da wata mata a waje.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel