Ta Faru ta Kare, Manyan Arewa Sun Hakura da Shiga Zanga Zanga, Sun ba Matasa Shawara
- Kungiyar Arewa Consultative Forum (ACF) ta ce ba za ta shiga cikin zanga-zangar yunwa da ake shirin farawa daga ranar Alhamis ba
- Kungiyar manyan Arewan ta yi nuni da cewa manufar zanga-zangar ba ta shafi babbar matsalar tsaro da ta addabi yankin Arewa ba
- A yayin da ta zayyana dalilanta na kin shiga zanga-zangar, ta yi kira ga gwamnati da ta dauki matakan kawo sauki ga rayuwar 'yan kasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Kungiyar manyan Arewa ta ACF ta tsame hannunta daga zanga-zangar da aka shirya gudanarwa na tsawon kwanaki 10 a fadin kasar nan.
Sanarwar matsayar Arewa Consultative Forum kan zanga-zangar ta fito ne ta hannun Farfesa Tanko Muhammad-Baba, sakataren yada labaran kungiyar na kasa.
Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan yada labarai, Bayo Onanuga ne ya wallafa sanarwar a shafinsa na X a ranar Talata, 30 ga Yulin 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Manyan Arewa sun fice daga zanga-zanga
Sanarwar ACF ta ce:
“Kungiyar ACF ta sa ido sosai a kan manufofin da suke tattare da shirya zanga-zangar yunwa, wadda wasu da ba a san ko su waye ba za su jagoranta.
“Bayanan da ke yawo a intanet sun danganta zanga-zangar da rashin gamsuwa da tsadar rayuwa da ta addabi kasar sakamakon wasu tsare-tsaren gwamnatin Bola Tinubu.
"Yayin da take amincewa da 'yancin da tsarin mulki ya ba 'yan Najeriya na yin zanga-zanga, ACF ta yi hannun riga da wannan shiri na yin zanga-zangar yunwar."
Meyasa manyan Arewa hakura da zanga-zangar?
ACF ta zayyana dalilai da dama na adawa da zanga-zangar kamar rashin tuntubar manya game da rikon amana da gudanar da mulki da kuma rashin fayyace buƙatun masu zanga-zangar.
Kungiyar ta kara da cewa kai tsaye wannan zanga-zangar ba ta kawo wata mafita ta magance matsalar rashin tsaro a Arewa ba.
Jaridar Vanaguard ta ruwaito ACF na cewa:
"Rufe kasar na kwanaki 10 zai wuce kima kuma ba zai yi tasiri ba, wanda akwai yuwuwar zanga-zangar ta rikide zuwa tashin hankali ko kuma 'yan ta'adda su fake da ita."
ACF ta bukaci matasa da su guji shiga zanga-zangar tare da yin kira ga gwamnati da ta saurari koken jama'a domin magance manyan matsalolin da suka addabi kasar.
Matasan Ibo sun kauracewa zanga-zanga
A wani labarin, mun ruwaito cewa matasan Ibo sun yanke shawarar ficewa daga cikin shirin zanga-zangar da ake shirin gudanarwa a farkon watan Agusta.
Kungiyar Ibo ta Ohanaeze Ndigbo ce ta sanar da hakan bayan ganawa da matasan kan matsalolin shiyyar Kudu maso Gabas.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng