NNPC Ya Aika Sako ga Ƴan Najeriya Yayin da Gidajen Mai Suka Fadi Sabon Farashin Fetur

NNPC Ya Aika Sako ga Ƴan Najeriya Yayin da Gidajen Mai Suka Fadi Sabon Farashin Fetur

  • Kamfanin man fetur na kasa (NNPC) ya fitar da bayani game da matsalar karancin man fetur da ta addabi Legas da Abuja
  • An ce karancin ya kai ga gidajen man suna sayar da man fetur a farashi mai tsada fiye da farashin da NNPC ke sayarwa
  • Legit Hausa ta fahimnci cewa 'yan kasuwar bumburutu suna sayar da litar fetur a kan sama da Naira 1,000 a wasu sassan kasar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Kamfanin NNPCL ya bayyana cewa karancin man fetur da ake fama da shi a halin yanzu ya samo asali ne sakamakon cikas a ayyukan wasu jiragen mai guda biyu.

A cewar NNPCL, matsalar da jiragen ruwan masu dauke da fetur din suka samu ya haifar da tangarda wajen samar da mai da kuma rarraba shi.

Kara karanta wannan

Sauki zai zo nan kusa: Siminti zai sauka, BUA ya gano hanyar sauke farashi kayansa a Najeriya

NNPC ya yi magana kan karancin fetur da kuma farashin mai a gidajen man kasar
Wahalar mai ta tsananta a Legas da Abuja, NNPCL ya fadi dalili. Hoto: Bloomberg/contributor
Asali: Getty Images

Olufemi Soneye, babban jami’in sadarwa na kamfanin NNPC, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a shafin NNPCL na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta bayyana cewa:

“NNPC na son bayyana cewa tangardar samar da man fetur da rarraba shi da aka samu a wasu sassa na Legas da kuma Abuja ya faru ne sanadin cikas da aka samu a ayyukan wasu jiragen ruwa guda biyu.
"Kamfanin ya kuma bayyana cewa yana aiki ba dare ba rana tare da masu ruwa da tsaki domin magance lamarin tare da dawo da rarraba man kamar yadda aka saba."

Gidajen mai sun sauya farashi

A halin da ake ciki kuma, gidajen mai sun kara farashin man fetur sakamakon cunkoson layuka da kuma karancin fetur din da aka samu a Legas.

Kara karanta wannan

Abubuwa 7 da suka jawowa gwamnatin Tinubu zanga zanga bayan shekara 1

An rahoto cewa, baya ga gidajen man NNPC da ke sayar da da lita a kan N650, sauran gidajen man ‘yan kasuwa na sayar da fetur din tsakanin N850 zuwa N950 kan kowace lita.

Da muka tuntubi wani Abdullahi Rabiu mazaunin Abuja, wanda ke sana'ar 'uber' ya ce a safiyar yau Lahadi ya sayi litar fetur kan N857 a gidan mai, a wajen 'yan bumburutu kuma N1,200.

A nan jihar Kaduna, da muka tuntubi manajan gidan man Bushara, Mubarak Mohammed, ya shaida mana cewa ba su da mai saboda gaza samun shi da suka yi, amma lita ta kai N865.

NNPCL zai nemo rancen $2bn

A yayin da wahalar man fetur ta tsananta a kasar, kamfanin NNPCL ya sanar da shirinsa na nemo rancen dala biliyan 2 domin inganta gudanar da ayyukansa.

Mun ruwaito cewa shugaban kamfanin, Mele Kyari ya ce NNPC za ta karbi bashin ne a kan hako ganga 30,000-35,000 kowace rana amma bai fadi adadin da ake nema ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.