Najeriya Ta Samu Matsala a Gasar Olympics, an Kama ’Yar Dambe Tana Tu'ammali da Kwaya

Najeriya Ta Samu Matsala a Gasar Olympics, an Kama ’Yar Dambe Tana Tu'ammali da Kwaya

  • An dakatar da ‘yar wasan damben Najeriya, Cynthia Ogunsemilore daga gasar Olympics bayan gwaji ya nuna tana tu'ammali da kwaya
  • Hukumar ITA gwajin jinin da aka yiwa Cynthia ya nuna cewa tana tu'ammali da kwayar furosemide wadda ke kara kuzari a jiki
  • Sai dai an ce 'yar damben na da 'yancin ta kalubalanci dakatarwar a kotun sasantawa kuma tana iya neman sake gwajin jinin na ta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Paris - Hukumar da gwaje-gwajen kwayoyi ta kasa da kasa ta sanar da cewa an dakatar da 'yar wasan damben Najeriya Cynthia Temitayo Ogunsemilore daga gasar Olympics.

Gwajin da aka yiwa 'yar damben"ya nuna cewa akwai sinadarin kwayar furosemide a jinita, wadda aka haramtawa 'yan wasa amfani da ita," inji sanarwar ITA a ranar asabar.

Kara karanta wannan

Abubuwa 7 da suka jawowa gwamnatin Tinubu zanga zanga bayan shekara 1

Hukumar ITA ta sanar da sakamakon binciken gwajin kwayar 'yar damben Najeriya, Cynthia
Hukumar ITA ta dakatar da 'yar damben Najeriya Cynthia bayan ta fai gwajin kwaya. Hoto: @dekunleshola
Asali: Twitter

An ce Furosemide na ƙarƙashin "kwayoyin kara juriya da boye gajiya" na kundin hukumar yaƙi da amfani da kwayoyin kara karfin 'yan wasa ta Duniya (WADA), inji rahoton Channels.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An dakatar da Cynthia daga Olympics

An ranar Alhamis ne aka debi jinin 'yar wasan a birnin Paris, kwana guda gabanin bikin bude gasar Olympics, kuma wani dakin gwaje-gwaje da WADA ta amince da shi ya fitar da rahoton a ranar Asabar.

Sanarwar hukumar ITA ta ce:

"An sanar da 'yar wasan game da lamarin kuma an dakatar da ita na wani dan lokaci har sai an samo bakin zaren lamarin a hukumance.
"Wannan yana nufin cewa an dakatar da ita daga yin wasa, yin horo, koyarwa, ko shiga kowane irin aiki, yayin wasannin Olympics na Paris 2024."

Cynthia na iya daukaka karar gwajin

Kara karanta wannan

Harkar noma: Gwamnatin Kano ta ware biliyoyi domin aikin madatsar ruwa

Jaridar The Guardian ta ruwaito cewa Ogunsemilore na da hakkin ta kalubalanci dakatar da ita da aka yi a kotun sasantawa kuma tana iya neman sake bincike kan samfurin jinin na ta.

'Yar damben da ke a rukunin masu nauyin kasa da kilo 60, mai shekaru 22 za ta fara wasanta a gasar Olympics ranar Litinin, sai kuma ga wannan lamari ya faru.

Wannan ci gaban ya kara kawo cikas ga ‘yan wasan damben Najeriya, inda ya bar Adam Olaore a matsayin daya tilo da ke fatan samun lambar yabo ga al’ummar kasar.

'Yan wasan da aka dakatar saboda kwaya

A wani labarin, mun ruwaito cewa an dakatar da Paul Pogba, tsohon dan wasan Manchester United daga buga kwallon kafa na tsawon shekaru hudu bayan da ya fadi gwajin kwayoyi.

Sai dai ba wai Pogba bane kadai dan wasan da aka taba dakatarwa saboda samun kwaya a jininsa ba, mun tattaro jerin 'yan wasanda suka taba faduwa gwajin kwayoyin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.