Za’a gudanar da wasan damben gargajiya na bana a jihar Sakkwato

Za’a gudanar da wasan damben gargajiya na bana a jihar Sakkwato

Bababn sakataren hukumar shirya wasan damben gargajiya na kas,a Ahmed Jada ya bayyana cewa gasar dambe na bana zai gudana ne a jihar sakkawato, watan gobe, inji rahoton kamfanin dillancin labaru, NAN

Jada ya bayyana haka ne a ranar Litinin 27 ga watan Nuwamba a birnin Abuja, inda yace damben na bana za’a gudanar da shi ne a filin kasuwar duniya na jihar Sakkwato, dake titin tsohon filin jirgin sama.

KU KARANTA: Hotunan wani gwabzawa da aka yi tsakanin jami’an tsaro da Boko Haram, an kashe yan ta’adda 10

Majiyar Legit.ng ta ruwaito da fari, jihar Kebbi ce zata dauki nauyin damben, amma daga bisan saboda karancin wajen wasa aka matsar da shi zuwa jihar Sakkwato, inda a yanzu duk wani shiri ya kammala na karbar bakoncin jihohi takwas da zasu fafata.

Za’a gudanar da wasan damben gargajiya na bana a jihar Sakkwato
Madambata

“Wannan it ace hanya mafi inganci na habbaka wasan damben gargajiya, kuma jihojin Katsina, Neja, Kano, Kebbi, Nassarawa, Kaduna, Ogun da FCT ne zasu fafata” Inji shi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng