Gasar Olympics: Dalilai (5) da suka sa aka yi waje da Najeriya

Gasar Olympics: Dalilai (5) da suka sa aka yi waje da Najeriya

Gasar Olympics: Dalilai (5) da suka sa aka yi waje da Najeriya

Kungiyar kwallon kafar U-23 ta Najeriya sun sha kashi hannun Kasar Jamus da ci biyu da nema a wasan kusa da karshe a Gasar Olympics na RIO 2016. Ko me ya jawo aka doke Najeriyar?

Kasar Jamus ta doke Dream Team ta Najeriya da ci 2-0 a wasan daf da karshe na Gasar Olympics.

AN KWACE TSAKIYA:

Dalilin farko da ya sa aka samu galaba kan Najeriya shine Jamus ta karbe tsakiya a wasan. Don haka suka rike kwallon, suka kuma hana Mikel Obi sakat. Idan aka raba ka da tsakiyar ka, an gama cin ka wasa.

RASHIN DAN WASA AZUBUIKE A TSAKIYA:

Najeriya tayi rashin dan wasan tsakiyar nan Azubuike a fili, dan wasan bai buga wasan ba saboda katin da ya dauko a wasannin baya. Rashin dan wasan ya sa aka sanya wani Ndifreje Udo mai shekaru 19, dama ai tsintaciyar mage ai ba ta mage. Wannan ya kara ma Mikel aiki a tsakiya, ya kuma taimaka wajen hana Najeriya zuwa wasan karshe.

KURA-KURE DA DAMA:

‘Yan wasan Najeriyan sun ta tafka kuskure da dama a wasan, hakan kuma ya sa izzar ‘yan kwallon duk da ta ragu a wasan. ‘Yan wasan Najeriya irin su Shehu da Amuzie sun ta tafka kuskure a cikin wasan wajen mika kwallaye, wannan abu ya wahalar da su Ezekiel da Umar da ke gaba.

RASHIN KAI HARI GIDAN JAMUS:

Damar kirkin da Najeriya ta samu a wasan shine wani yunkuri na Mikel Obi, Kyaftin din yayi kokari har ya auna Golan na Jamus. In ban da wannan Najeriya ba ta tabuka komai ba a gidan Jamusawan, asali ma Ezekiel bai yi komai ba a wasan, aka kuma hana Sadiq Umar wani abu, ba kuma a maganar su Aminu Umar ma.

HATSABIBAN JAMUSAWA:

Maganar gaskiya kuma shine Kasar Jamus na da ‘yan wasa, kwararru kuma hatsabibai irin su Gnarby da Selke dsr. Ga shi kuma babban dan wasan Najeriya Etabo, rauni ya hana sa buga wasan.

KU KARANTA: OLYMPICS: YAR NAJERIYA TA KAI ZAGAYE NA GABA

 

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng