Sunayen Sanatoci da ‘Yan Majalisar Tarayya 6 da Mutuwa ta Dauke Bayan Cin Zaben 2023

Sunayen Sanatoci da ‘Yan Majalisar Tarayya 6 da Mutuwa ta Dauke Bayan Cin Zaben 2023

Abuja - Makoki ake yi a majalisar tarayya a halin yanzu a sakamakon rasuwar Sanata mai wakiltar mutanen kudancin jihar Anambra.

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Kafin Ifeanyi Ubah, wasu ‘yan majalisar tarayya sun rasu a wannan majalisar, watanni kadan bayan sun yi nasara a zaben 2023.

Jaridar Daily Trust ta yi kokari wajen yin waiwaye, ta tattaro ‘yan majalisar da aka rasa a cikin shekara guda da kafa gwamnati.

'Yan majalisa
An rasa mutane 6 a majalisar tarayya daga 2023 zuwa 2024 Hoto: Nigerian Senate/House of Representatives, Federal Republic of Nigeria
Asali: Facebook

'Yan majalisa da Sanatoci da suka rasu:

1. Majalisa ta rasa Ifeanyi Ubah

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tun da safiyar Asabar, Sahara Reporters ta kawo labarin mutuwar Sanata Ifeanyi Ubah a birnin Landan inda yake neman magani.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi magana mai jan hankali bayan mutuwar sanatan APC, ya yi addu'a

Sanata Ifeanyi Ubah ya ga mutuwa kiri-kiri kwanakin baya amma ya tsira da ransa. Kwanan nan ya sauya sheka daga YPP.

Ana tunanin ya shigo APC ne da niyyar ya nemi takarar gwamnan Anambra a zaben 2025.

2. Ekene Adams ya tafi

Ba a dade da kawo rahoto cewa Hon. Ekene Adams mai wakiltar Chikun/Kajuru a majalisar wakilan tarayya ya riga mu gidan gaskiya ba.

Wani mazaunin jihar Kaduna ya shaida mana yadda Ekene Adams ya yi ta fama da rashin lafiya, ya ce mazabarsa tayi babban rashi.

Saboda yadda yake harkar kwallon kafa, marigayin ya shahara musamman tsakanin matasa har a wajen mazabar Chikun/Kajuru.

3. Hon. Olaide Akinremi

A watan Yulin nan ne aka rasa Hon. Olaide Akinremi mai wakiltar mazabar Ibadan ta Arewa a majalisar wakilan tarayya a inuwar APC.

Olaide Akinremi (Jagaban) wanda ya kasance shugaban kwamitin cibiyoyin nazarin kimiyya a majalisa ya bar duniya yana da shekara 51.

Kara karanta wannan

Rai baƙon duniya: Majalisar Dattawa ta sanar da mutuwar fitaccen sanatan APC

4. Mutuwar Isa Dogonyaro a majalisa

Watanni biyu kafin mutuwar Jagaban, aka wayi gari da labarin rasuwar Isa Dogonyaro mai wakiltar mutanen Garki/Babura a majalisar kasa.

Hon. Isa Dogonyaro ya zama ‘dan majalisa ne bayan kotu ta tsige Aminu Kanta. Mutane da-dama a Facebook sun kadu da jin labarin rasuwar.

5. Abdulkadir Jelani Danbuga

A watan Oktoban 2023 Leadership ta rahoto cewa Abdulkadir Jelani Danbuga mai wakiltar Sabon Birni da Isa a majalisar wakilai ya bar duniya.

Abdulkadir Jelani Danbuga wanda ya fito daga Sokoto ya yi rashin lafiya kafin ajali ya yi kira. ‘Dan siyasar ya bar mata biyu da ‘ya da jikoki.

6. Yaron Sarki ya rasu a majalisa

Bai wuce watanni biyu a majalisa ba, sai aka ji mutanen Jalingo/Yorro/Zing sun rasa wakili a Abuja, Ismaila Maihanci ya rasu yana shekara 36.

Kafin zamansa ‘dan majalisar tarayya yana matashi, Hon. Ismaila Maihanci ya baba gwamnan Taraba shawara kuma ya yi sakataren PDP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng