Yadda Gwamnati Ta Kashe Naira Tiriliyan 2.36 Wajen Yaki da Barayin Mai a Shekara 4
- Gwamnatin tarayya ta ce ta kashe sama da Naira tiriliyan 2.36 daga shekarar 2020 domin yaki da masu satar danyen mai a kasar
- Sakataren gwamnatin tarayya, George Akume wanda ya bayyana hakan ya ce an yi amfani da wani bangare na kudin kan alkinta man
- Majalisar wakilai ta kafa wani kwamiti da zai binciki asarar da aka tafka a bangaren mai da iskar gas sakamakon barayin man
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Gwamnatin tarayya ta kashe sama da dala biliyan 1.5 daga shekarar 2020 zuwa yau domin kare gidajen man kasar da kuma dakile satar danyen mai.
Sakataren gwamnatin tarayya, George Akume ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis a wajen taron jin ra’ayin jama’a na majalisar wakilai kan satar danyen mai.
Gwamnati ta yi magana kan satar mai
Akume ya samu wakilcin babban sakatare, a ayyukan bai daya na tarayya, Maurice Nandi, kamar yadda rahoton Channels TV ya nuna.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sakataren gwamnatin ya ce gwamnatin tarayya ta damu da wani rahoto da hukumar kula da masana’antu ta Najeriya (NEITI) ta fitar na kwanan baya.
Cibiyar binciken ICRI ta ruwaito hukumar NEITI ta bayyana cewa an sace danyen mai da ya kai darajar sama da dala biliyan 46 (Naira tiriliyan 72.6).
An yi wannan aika aika ne tsakanin shekarar 2009 zuwa 2020, watau shekaru sama 10 kenan.
"Najeriya ta tafka asarar $10bn" - Majalisa
Majalisar dai ta kafa kwamiti na musamman karkashin jagorancin Ado Doguwa, domin ya binciki asarar da aka yi a bangaren mai da iskar gas.
Har ila yau, kakakin majalisar, Tajudeen Abbas ya ce an yi asarar dala biliyan 10 a cikin watanni bakwai na satar danyen mai kuma ba abin da aka iya yi har yanzu.
Majalisa ta gamsu da dizal din Dangote
A wani labarin, mun ruwaito cewa majalisar wakilai ta fitar da rahoton binciken da ta yi kan ingancin dizal din da matatar man Dangote ke sayarwa a Najeriya.
A yayin da yake gabatar da rahoton, Hon. Esosa Iyawe ya ce sun gano dizal din Dangote ya fi inganci kan wanda ake shigo da shi daga kasashen ketare.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng