Dakarun soji sunyi wa wasu barayin danyen mai laga-laga bayan musayar wuta mai zafi

Dakarun soji sunyi wa wasu barayin danyen mai laga-laga bayan musayar wuta mai zafi

- Sojojin Najeriya da ke atisayen Operation Delta Safe sunyi arangama da wasu masu fasa bututun man fetur a Delta

- Hukumar sojin kuma ta karyata labaran da ake yadawa na cewa sojojin sunci mutuncin al'ummar yankin

- Sai dai wani mazaunin yankin ya yi ikirarin cewa sojojin sun keta hakkin mutane yayin da suka tafi wasu kauyuka neman masu satar man fetur

Sojojin hadin gwiwa JTF wanda aka sauya zuwa rundunar Operation Delta Safe sunyi musayar wuta da wasu wanda ake zargin barayin man fetur a wasu garuruwa da ke Warri , kudu maso yammacin jihar Delta.

Sojojin hadin gwiwa sunyi musayar wuta da barayin man fetur a kudu
Sojojin hadin gwiwa sunyi musayar wuta da barayin man fetur a kudu

Mai magana da yawun rundunar ta yankin Neja Delta, Manjo Ibrahim Abdullahi ya shaidawa Vangaurd cewa an daura musu alhakin kare kayayakin gwamnati da ke yankin.

KU KARANTA: Sultan ya yi kaca-kaca da wani gwamna da tsohon minista a kan alakanta kisan makiyaya da Danfodio

Ya kuma kara da cewa babu kanshin gaskiya cikin jita-jitan da wasu ke yadawa ne cewa sunci mutuncin mutane a yankin a yayin da suke gudanar da atisayen su na kwanaki biyu a yankin.

"Ya zama dole mu rika kulawa da irin bayanan da ake yadawa, aikin mu shine kulawa da kayayakin man fetur da iskan gas da kuma kawar da yan tsagera. Mun zo ne domin mu kare bututun man fetur da kuma al'umma."

Sai dai wani mazaunin yankin mai suna Mr Mike Ikima ya ce wasu daga cikin sojojin hadin gwiwar ta JTF sun tafi shiga unguwanin Okerenkokogbone da Opuede inda suke naman masu satar man fetur, inda kuma ya ce sojojin sun ci mutuncin mutanen garin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel