Abin da Ya Sa Ba Za a Taba Samun Zaman Lafiya a Najeriya Ba, Kungiyar Ibo Ta Magantu

Abin da Ya Sa Ba Za a Taba Samun Zaman Lafiya a Najeriya Ba, Kungiyar Ibo Ta Magantu

  • Ƙungiyar Ohanaeze Ndigbo ta yi ikirarin cewa Najeriya ba za ta taba samun zaman lafiya da cigaba ba tun da ana yi masu rashin adalci
  • Mai magana da yawun ƙungiyar, Chiedozie Ogbonnia, ya ce matsin rayuwar da ake ciki sakamako ne na wariya da cutar dasu da ake yi
  • Sanarwar da ƙungiyar ta fitar ta bayyana cewa ba yanzu aka fara musu rashin adalci ba, an yi musu tun zamanin mulkin Buhari

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Ƙungiyar zamantakewa da al'ada ta Ibo, Ohanaeze Ndigbo ta ce Najeriya ba za ta fuskanci zaman lafiya da cigaba ba saboda yadda ake yi wa Ibo rashin adalci.

Igbo ƙabila ce da tafi yawa a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya.

Kara karanta wannan

Ganduje ya gurgunta shirin Obi, sanatan jam'iyyar Labour ya sauya sheka zuwa APC

Kabilar Ibo sun yi magana kan zaman lafiya a Najeriya
Kabilar Ibo sun yi ikirarin cewa Najeriya ba za ta taba samun zaman lafiya ba. Hoto: @Ohanaezendigboo
Asali: UGC

"Dalilin rashin zaman lafiya a Najeriya" - Ibo

Mai magana da yawun ƙungiyar Ohanaeze Ndigbo, Chiedozie Ogbonnia, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, Premium Times ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Ohanaeze Ndigbo tana tsaye gam kan cewa ba za a taba samun zaman lafiya, cigaba da haɓakar kasar nan ba ma damar tsarukan gwamnati na cutar da ƙabilar Ibo."

- A cewar Chiedozie Ogbonnia

A yayin bada misali na zargin rashin adalci, Ogbonnia ya tuna lokacin da tsohon Shugaba Muhammadu Buhari, a watan Janairun 2021 ya naɗa hafsoshin tsaro amma babu ɗan ƙabilar Ibo.

‘Matsin rayuwa, rashin adalci ga Ibo'

Ogbonnia ya kwatanta halin matsin tattalin arzikin da ake ciki a Najeriya matsayin alhakin ƙin Ibo da ake yi, inji rahoton Arise News.

Ya kara da cewa:

"Wannan sakamako da ba za a iya gujewa ba na rashin adalci, wariya, haɗin kai wurin cuta da warewar ƙabilanci da ake wa Ibo."

Kara karanta wannan

Jarumar fim ta fallasa 'alaƙar' da ke tsakaninta da shugaban majalisar dattawa, Akpabio

Ba wannan ba ne karon farko da Ibo ke zargin gwamnatin tarayyar Najeriya da yi mata rashin adalci.

Tun bayan yaƙin basasa tsakanin 1967 da 1970, 'yan ƙabilar Ibo sun cigaba da ƙorafi kan cewa ana ware su yayin rarraba ababen more rayuwa da ma muƙaman siyasa.

Fushin Ibo kan faduwar zaben Obi

Fusatar Ibo ta cigaba bayan zaben 2023 na shugaban ƙasa yayin da Peter Obi, wanda ɗan ƙabilar ne ya gaza nasara a zaben duk da yana da masoya masu yawa.

Obi tsohon gwamnan Anambra, shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar Labour Party.

Ya ƙalubalanci nasarar Bola Tinubu a zaben a kotuna da dama na Najeriya, har zuwa kotun ƙoli inda yayi faɗuwar ƙarshe.

Tinubu ya magantu kan zanga-zanga

A wani labari na daban, mun ruwaito muku cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci 'yan Najeriya da su hakura da fitowa zanga-zangar da ake shiryawa.

Kara karanta wannan

Yaki zai dauki zafi, sojoji sun bankado babban abin da ya kawo 'yan bindiga Arewa

Ya sanar da hakan ne yayin ganawa da majalisar sarakunan gargajiya waɗanda suka buƙaci matasa da su yi haƙuri kuma a tattauna matsalolinsu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.