Bincike ya nuna yadda kasar Bayafara ta faro

Bincike ya nuna yadda kasar Bayafara ta faro

-Kalmar Biafra ta samo asali ne daga gabar mashigin tekun Atlantic da ke yankin Kudu maso Gabashin Najeriya

-Fafutikar neman kafa Jamhuriyar Biafra ne dalilin aukuwar yakin basasa a Najeriya

-Nnamdi Kanu ne ya sake dago da batun Biafra

Ga dukan mai sauraren kafafun yadda labarai, Kalmar Biafra ba sabuwar kalma bane a kunnuwansa. Masu amfani da wannan kalma dai sune wasu mutane masu fafutikar ballewa daga Najeriya wanda mafi yawancin su yan kabilar ibo ne da ke yankin kudu maso gabashin kasan.

Sunnan Biafra ya samo asali ne daga mashigin tekun Atlantic da ke yankin Kudu maso Gabashin Najeriya.

Ko da yake galibin mutanen da ke zaune a yankin yan kabilar igbo ne, akwai wasu kabilun da suka hada da Ijaw, Eket, Ibibio, Efik, Ejagham da Annang.

Bincike ya nuna Yadda kasar Bayafara ta faro
Bincike ya nuna Yadda kasar Bayafara ta faro

Yakin basasar kasar ya faru ne bayan da masu fafutikan neman kafa kasar Biafran suke bada sanarwan ballewa daga Najeriya, da kuma kafa tasu kasar da suka sa ma suna ”Jam'uriyar Biafra”. Wannan sanarwan ya fito ne daga bakin jogoran masu neman kafa kasar Biafran a ranar 30 ga watan Mayu 1967 mai suna Laftanal Kanar Chukwuemeka Odumegwu.

Kafin yakin basasar anyi juyin mulki guda biyu a kasar, na farko shine wanda aka yi a watan Janairu na 1966 inda aka kasha Farai Ministan farko na kasar Sir Abubakar Tafawa Balewa da Firimiyar Jihar Arewa Sir Ahmadu Bello da ma wasu jagororin arewa da kuma na Yarbawa, amma ba’a kasha Shugaban yankin igbo ba.

KU KARANTA KUMA: Dangote ya mayar da martani kan zargin rashawa

Na biyu kuma shine juyin mulkin da wasu sojijin arewa suka yi wa gwamnatin Janar Aguiyi Ironsi wanda dan kabilar igbo ne. Wannan ya ingiza gaba tsakanin muatenen yankin arewa da kudu.

An kwashe shekara biyu da rabi ana gwabza yaki tsakanin sojojin Najeriya da na Biafra, amma a ranar 15 ga watan Janairun na 1970, jagororin sojojin Biafran suka ajiye makamai suka mika wuya ga dakarun Najeriya. Kanar Ojukwu ya tsere zuwa kasar Ivory Coast amma daga baya ya dawo Najeriya bayan gwamnatin Shugaba Shagari tayi masa afuwa. Ojukwu ya rasu a ranar 1 ga watan Maris na shekarar 2012.

Kabilar sun ci gaba da sama tare da yan Najeriya tun wannan lokacin kwatsam sai wani mutum Nnamdi kanu wanda nan kabilar igbo ne mazaunin kasar Birtaniya ya sake dago da batun, yana tuhuman gwamnatin Najeriya da nuna wariya wajen al’amuran da suka shafi cigaban kasar. Kanu ya kafa kungiyar da ya kira Indegenous People of Biafra, IPOB wanda manufan ta shine kafan kasan Biafran.

Sai dai fafutikan nasa baiyi karfi ba sai bayan zaben Shugaba Buhari a matsayin shugaban kasa a shekara ta 2015, Kanu yana amfani da gidan rediyon sa da ya kafa ba bias ka’ida domin yadda manufan sa da kuma sukar gwamnatin Najeriya musamman mutanen arewa.

Daga baya gwamnati ta sa an rufe gidan rediyon kuma ta kama Nnamdi Kanu akan zargin shi da yi ma kasa zagon kasa. Bayan shafe sama da watanni 18, kotu ta bada belin Nnamdi Kanu amma bi sa ga dukkan alamu har yanzu yana kan bakan sa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel