Da duminsa: Peter Obi ya zabi Kirista, dan Kudu matsayin mataimakinsa

Da duminsa: Peter Obi ya zabi Kirista, dan Kudu matsayin mataimakinsa

  • Mai nema zama shugaban kasa a 2023 karkashin jam'iyyar LP, Peter Obi, ya zabi Doyin Okupe matsayin abokin tafiyarsa
  • Peter Obi, wanda yayi murabus daga PDP ana jajibirin zaben fidda gwani ne jam'iyyar Labour Party ta tsayar
  • Doyin Okupe ya kasance na hannun daman tsohon shugaban kasa, Goodluck Ebele Jonathan

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Tsohon mai magana da yawun shugaban kasa, Doyin Okupe, a ranar Juma'a ya bayyana cewa shine aka zaba matsayin mataimakin dan takarar shugaban kasar jam'iyyar Labour Party, Peter Obi.

Doyin Okupe ya bayyana hakan a hirarsa da Seun Okinbaloye na tashar ChannelsTV.

Peter Obi ya bi sahun Tinubu wajen zaben mai addini daya da shi matsayin abokin tafiya.

Amma ana hasashen cewa an sanya sunan Okupe ne kawai don kada wa'adin INEC ta cika, daga baya akwai yiwuwa a sauya sunansa.

Kara karanta wannan

Wike Ya Saki Hoto Da Magana Mai Boyayyen Ma'ana Bayan Jita-Jitar Ganawarsa Da Tinubu a Faransa

Peter Okupe
Da duminsa: Peter Obi ya zabi Kirista, dan Kudu matsayin mataimakinsa
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Asali: Legit.ng

Online view pixel