Ambaliyar Ruwa Ta Yi Babbar Barna a Jihar Arewa, Mutum 1,664 Sun Rasa Matsugunni
- Mutane 1,664 ne suka rasa gidajensu a wasu yankunan jihar Sokoto sakamakon mamakon ruwan saman da aka fara tun ranar Talata
- Ruwan saman ya wawushe gonakin jama'a a wasu kauyukan Dantudu, Balakozo, Gidan Tudu da Tsitse towns, da sauransu
- Jami'in bayanai na SEMA a Sokoto, Abdullahi Ghani, ya sanar da yawan gidaje da magidantan da lamarin ya shafa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Sokoto - An ruwaito cewa kusan mutane 1,664 ne suka rasa matsugunansu a yankuna huɗu dake ƙaramar hukumar Gada ta jihar Sokoto sakamakon ambaliyar ruwa.
Jami'in hulda da jama'a na hukumar agajin gaggawa na jihar Sokoto, Abdullahi Ghani ya ce ambaliyar ruwan ta faru ne sakamakon mamakon ruwan sama da aka yi a yankin.
Ghani ya ce ambaliyar ruwan ta lalata gonaki masu tarin yawa, kamar yadda jaridar Punch ta bayyana.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Ruwan saman da aka yi ya faru ne a ranar 17 ga watan Yulin 2024 kuma ya jawo mazauna ƙaramar hukumar Gada ta jihar Sokoto sun rasa matsugunni.
“Ya lalata hektoci da dama na gonaki tare da halaka tumaki da akuyoyi masu tarin yawa.
"An gano wannan ne yayin da jami'an hukumar NEMA da SEMA suka yi ziyarar duba halin da ake ciki a jihar."
- A cewar Abdullahi Ghani.
Sunayen ƙauyukan da ambaliyar ta shafa
Jaridar Tribune ta ruwaito mai magana da yawun hukumar ya ƙara da cewa:
"A ƙauyen Dan Tudu, gidaje 62 da magidanta 71 lamarin ya shafa, yayin da ƙauyen Balakozo, gidaje 33 da magidanta 48 ambaliyar ta shafa.
“A kauyen Gidan Tudu kuwa, jimillar gidaje 38 da magidanta 52 abun ya ritsa da su. A garin Tsitse, jimillar gidaje 68 da magidanta 89 lamarin ya shafa."
"Jimillar mutanen da lamarin ya shafa a Dan Tudu, Balakozo, Gidan Tudu da garin ya kai 1,664."
Gwamnati ta fadi inda za ayi ambaliyar ruwa
A wani labari na daban, mun ruwaito muku cewa gwamnatin tarayya ta bayyana sunayen jihohin da za a iya fuskantar ambaliyar ruwa.
A don haka ne gwamnatin tarayyar tayi kira ga jama'a mazauna kwari da wuraren da lamarin zai iya shafa da su kauracewa yankunan.
Asali: Legit.ng