Hotuna: Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 14 a Zamfara, ta kwashe gada a Sokoto

Hotuna: Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 14 a Zamfara, ta kwashe gada a Sokoto

A kalla mutum 14 suka rasa rayukansu yayin da gidaje masu tarin yawa suka rushe bayan ambaliyar ruwa da ta auku a karamar hukumar Gummi ta jihar Zamfara a makon da ya gabata.

Jaridar SaharaReporters ta gano cewa, daruruwan mazauna yankin a halin yanzu sun zama 'yan gudun hijira.

Hotuna: Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 4 a Zamfara, ta kwashe gada a Sokoto
Hotuna: Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 4 a Zamfara, ta kwashe gada a Sokoto. Hoto daga TVC
Source: Twitter

Wani mazaunin yankin, ya ce babban mai bada shawara na musamman a kan harkokin tallafi da jin kai na Gwamna Bello Muhammad Matawalle, ya ziyarci yankin kuma ya rarraba kayan abinci ga wadanda lamarin ya shafa.

Ya danganta wannan ibtila'in ambaliyar ruwan da rashin tituna masu kyau a yankin.

Hotuna: Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 4 a Zamfara, ta kwashe gada a Sokoto
Hotuna: Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 4 a Zamfara, ta kwashe gada a Sokoto. Hoto daga TVC
Source: Twitter

"Mutum 14 sun rasu. Na gansu da idona kuma na ga gidajensu. Gidajen da ruwa ya wuce da su sun kai daruruwa.

KU KARANTA: Hotuna: Ma'aikatan da suka yi murabus sun hana shiga da fita a gidan gwamnatin Delta

Zamfara: Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 4, mutane da yawa sun rasa gidajensu
Zamfara: Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 4, mutane da yawa sun rasa gidajensu. Hoto daga SaharaReporters
Source: Twitter

"Babban mai bada shawara a kan harkokin jin kai da tallafi ga gwamnan jihar Zamfara, ya ziyarci yankin kuma ya kawo tallafin kayayyakin abinci ga jama'ar.

Hotuna: Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 4 a Zamfara, ta kwashe gada a Sokoto
Hotuna: Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 4 a Zamfara, ta kwashe gada a Sokoto. Hoto daga TVC
Source: Twitter

"Ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta yi iyakar kokarinta wurin samar da tallafi garesu. Abun tsoron shine idan bamu da gidaje kuma ba a gyara mana makarantu ba, dole mu bar yankin," majiyar tace.

Hotuna: Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 4 a Zamfara, ta kwashe gada a Sokoto
Hotuna: Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 4 a Zamfara, ta kwashe gada a Sokoto. Hoto daga TVC
Source: Twitter

KU KARANTA: Yadda jami'ai suka yi wa matashiya fyade a motar kaita asbiti bayan kamuwa da korona

A daya bangaren, wata babbar gada a jihar Sokoto ta fada sakamakon mamakon ruwan saman da aka tafka.

Mazauna yankin Margai da ke karamar hukumar Kebbe a jihar Sokoto sun kasance a gefe daya na jihar tun bayan da ambaliyar ruwan saman ta yi awon gaba da gadar da ta hada su da sauran jihar.

Hotuna: Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 4 a Zamfara, ta kwashe gada a Sokoto
Hotuna: Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 4 a Zamfara, ta kwashe gada a Sokoto. Hoto daga TVC
Source: Twitter

A wani labari na daban, hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Jigawa, SEMA, ta sanar da cewa yawan mutanen da suka mutu ya kai 2 tare da dubban gidaje da gonakin da suka lalace sakamakon gagarumar ambaliyar da ta auku a jihar.

Hotuna: Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 4 a Zamfara, ta kwashe gada a Sokoto
Hotuna: Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 4 a Zamfara, ta kwashe gada a Sokoto. Hoto daga TVC
Source: Twitter

Sakataren hukumar, Mr Yusuf Sani Babura, ya sanar wa manema labarai a Dutse cewa ambaliyar, wanda ke aukuwa duk shekara, ya shafi 17 daga cikin kananan hukumomi 27 na jihar wanda hakan ya jefa rayukan jama'a mazauna garuruwan cikin rudani.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel