Mutane sun koma kwana a daji saboda ambaliyar ruwa a jihar Sokoto

Mutane sun koma kwana a daji saboda ambaliyar ruwa a jihar Sokoto

- An sake samun ambaliyar ruwa da ta mamaye wasu kauyukan jihar Sokoto

- Wuraren da abun ya shafa sune kananan hukumomin Ilela da Gada da Isa da Sabon Birni da Goronyo

- Ibtila’in ya kuma lalata albarkatun gona da mazauna yankin suka noma

Rahotanni sun kawo cewa cewa an sake samun ambaliyar ruwa da ta mamaye wasu kauyuka a kan iyakar Najeriya da Nijar, lamarin da ya tilasta wa jama’ar yankin kwana a dajin Allah bayan sun rasa muhallansu a jihar Sokoto.

Yankunan da ibtila’in ta shafa sun hada da na kananan hukumomin Ilela da Gada da Isa da Sabon Birni da Goronyo.

Mutane sun koma kwana a daji saboda ambaliyar ruwa a jihar Sokoto
Mutane sun koma kwana a daji saboda ambaliyar ruwa a jihar Sokoto
Asali: Facebook

Ibtila’in ya kuma lalata albarkatun gona da mazauna yankin suka noma, yayin da suka mika kokon baransu zuwa ga hukumomi don tallafa musu.

Shafin rfi Hausa ta rahoto cewa mutanen wannan yanki dai sun fara yin kaura zuwa daji inda anan suke kwana sakamakon wannan matsala.

KU KARANTA KUMA: 2019: Tsohon gwamnan Plateau, Jonah Jang zai bayyana kudirinsa na takarar shugaban kasa a yau

A wani lamari makamancin wannan, Legit.ng ta rahoto a baya cewa hukumar kula da muhali na jihar Kaduna (KEPA) ta yi gargadin cewa akwai yiwuwar samun ambaliyar ruwa a wasu sassan jihar inda ta gargadi wasu mutane da ke zaune a wasu unguwani su tashi daga gidajensu.

Ambaliyar ruwa ta mamaye gidajen mutane da dama a kananan hukumomi uku na jihar Kaduna sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka kwarara a daren ranar Alhamis.

Sakataren hukumar agaji na jihar (SEMA), Mr Ben Kurah ne ya bayyana hakan a yayin da ya kai ziyarar gani da ido a wuraren da lamarin ya shafa, ya kuma kara da cewa ba'a rasa rayyuka ba sakamakon ambaliyar.

Ya ce toshewar magudanun ruwa da kuma yin gine-gine a hanyar ruwa ne ya janyo afkuwar ambaliyar ruwan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel