Hisbah Ta Lalata Giyar Naira Miliyan 60 a Katsina, Ta Rufe Otel da Ake Aikata Baɗala

Hisbah Ta Lalata Giyar Naira Miliyan 60 a Katsina, Ta Rufe Otel da Ake Aikata Baɗala

  • Hukumar Hisbah ta jihar Katsina ta bayyana yadda ta kama tare da lalata giya da miyagun kwayoyi da suka kai darajar N60 miliyan
  • Hukumar ta kama wasu 'yan mata goma a wani otel da ake zargin ana fasikanci da su tare da wasu maza ashirin
  • Kwamandan hukumar na jihar Katsina, Aminu Usman, ya sanar da hakan a ranar Lahadi inda yace hakan ya faru a Funtua

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Funtua, Katsina - Hukumar Hisbah ta jihar Katsina ta ce ta lalata giya da ta ƙwace da sauran miyagun ƙwayoyi da suka kai darajar Naira miliyan 60 a ƙaramar hukumar Funtua ta jihar.

Kara karanta wannan

Ambaliyar ruwa ta yi babbar barna a jihar Arewa, mutum 1,664 sun rasa matsugunni

Kwamandan Hisbah na jihar, Aminu Usman, ya bayyana hakan ga Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Katsina a ranar Lahadi.

Hukumar Hisbah ta jihar Katsina ta lalata giyar Naira miliyan 60 a Funtua
Katsina: Hisbah ta rufe wani otel bisa zargin ana lalata a ciki, ta kona giyar N60m. Hoto: FuntuaTV
Asali: Facebook

Kamar yadda Usman ya bayyana, a ƙalla kiret din giya 1,750 tare da jarkoki 33 na giya da ba ta kamfani ba aka ƙwace tare da lalatawa a Funtua, Daily Nigerian ta bayyana.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukumar Hisbah ta cigaba da bayanin cewa, ƙoƙarin yana daga cikin wajibcin dake kanta na tabbatar da dabi'a ta gari a tsakanin jama'a a jihar.

Hisbah ta cafke mata a otel

Hukumar Hisbah ta samu korafi a reshenta na Funtua kan wani gida da ake aikata baɗala a wani otel dake kan titin Sokoto dake cikin garin Funtua.

Tuni jami'an hukumar suka zabura suka kai samame otel ɗin inda suka yi nasarar kama 'yam mata goma da ake girke ana fasikanci da su.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya zama na farko a Arewa da ya amince zai fara biyan ma'aikata N70,000

Hukumar ta hanzarta miƙa su hannun 'yan sanda tare da wasu maza ashirin da aka kama su tare da su domin a gudanar da bincike, kamar yadda hukumar ta wallafa a shafinta na Facebook.

Jim kadan bayan wannan samamen, hukumar ta sake komawa otel din ta garkame shi har zuwa lokacin da za ta kammala gudanar da bincike.

Hisbah ta yabawa Gwamna Radda

Shugan Hisbah ya yabawa ƙoƙarin jami'an hukumar, inda ya yi kira garesu da su kara mayar da hankali wurin tabbatar da sun sauke nauyin dake kansu.

Aminu Usman ya kuma nemi goyon baya daga shugabannin addinai a jihar domin samun nasarar hukumar, inda yace Hisbah ba ta wata ƙungiya bace ko ɓangare.

Kwamandan Hisbah ya yabawa Gwamna Dikko Radda kan cikakken goyon bayan da yake bai wa hukumar a yayin sauke nauyin dake kansu.

Hisbah ta ƙwace kwalaben gida 8600

A wani labari na daban, mun ruwaito muku cewa, hukumar Hisbah ta yi ram da wata mota maƙare da kwalaben gida 8600 tare da direbanta a Kwanan Dangora dake tsakanin jihar Kaduna da Kano.

Hukumar ta yi nasarar kama wasu 'yan mata a sassa daban-daban na jihar Kano dake karuwanci ciki har da waɗanda aka taba kamawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.