Khadimul islam: Ganduje ya rufe wani babban Otel a Kano, an kama masu karuwanci 19

Khadimul islam: Ganduje ya rufe wani babban Otel a Kano, an kama masu karuwanci 19

Gwamnatin Jihar Kano ta rufe wani fittacen Otel mai suna Mbanefo Holiday Inn da ke Abeokuta road a unguwar Sabon Gari da ke birnin Kano a ranar Alhamis bisa zarginsa da aikata abubuwan da suka sabawa doka.

Kamfanin dillancin labarai na kasa, NAN ta ruwaito cewa yayin rufe Otel din, an kama a kalla mutane 28 cikinsu har da karuwai 19 da kuwa wasu baki 'yan kasashen waje.

A hirar da ya yi da manema labarai jim kadan bayan rufe Otel din, Direktan Cibiyar Kula da yawan bude idanu na jihar, Alhaji Abdullahi Mu’azu-Gwarzo ya ce an rufe otel din ne saboda sabawa wasu dokokin jihar da tayi.

Ya ce watanni bakwai da suka gabata, Jami'an kula da shige da ficen mutane na kasa, (Immigration) sun kama wasu bakin haure 14 a otel din cikinsu har da 'yan kasar Chadi da Kamaru.

DUBA WANNAN: Zargin Madigo: Yadda Hadiza Gabon ta titsiye Amina Amal, ta rika zagba mata mari

An rufe wani fittacen Otel a Kano, an kama karuwai 19
An rufe wani fittacen Otel a Kano, an kama karuwai 19
Asali: Twitter

"Muna aiki ne karkashin umurnin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje saboda ayyukan laifi da ake aikatawa a otel din.

"Kwanaki tara da suka wuce, mun gayyaci mahukuntan otel din mun gargadi su bisa wasu ayyukan laifi da ake aikatawa. Idan muka bari aka cigaba da irin wannan laifin, Allah kadai ya san abinda zai faru a gaba," inji shi.

Ya ce otel din na bawa miyagu daga kasashen waje, kananan 'yan mata da sauran wadanda ake zargi da laifi mafaka.

Bugu da kari, ya ce masu otel din sun mayar da shi gidan karuwai inda ake bayar da hayan dakuna da kankanin lokaci domin ayi amfani da shi a tafi wanda hakan ya sabawa ka'idar aikin otel a jihar Kano.

Wasu daga cikin matan da aka kama a otel din sun shaidawa manema labarai cewa sun fito ne daga jihohin Kaduna, Borno da Nasarawa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164