Cikakken Bayanin Sanatoci 2 da Su ka Taba Samun Matsala Bayan Sun Soki Shugaban Kasa

Cikakken Bayanin Sanatoci 2 da Su ka Taba Samun Matsala Bayan Sun Soki Shugaban Kasa

  • A bayan nan Najeriya ta cika da labarin tsige Sanata Ali Ndume daga bulaliyar majalisar dattawa saboda sukar gwamnatin Tinubu
  • Ga Sanata Ndume, ba wannan ne karon farko da aka taba tsige shi daga mukaminsa saboda sukar shugaba ba, ko a 2017 hakan ta taba faruwa
  • Sai dai ba iya Sanata Ndume ne kadai dan majalisar dattawa da ya taba gamuwa da matsala saboda ya kalubalanci shugaban kasa mai ci ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Tsige Sanata Ali Ndume daga mukamin bulalar majalisar dattawa ya kara bankado da abin da ke faruwa a majalisar tarayyar kan masu sukar shugaban kasa mai ci.

Ba tun yanzu ake tsigewa ko dakatar da dan majalisar tarayya saboda ya nuna adawa da abin da ke faruwa ba, ko a lokacin Shugaba Olusegun Obasanjo, hakan ta taba faruwa.

Kara karanta wannan

Duk da rasa mukaminsa Sanata Ndume ya ci gaba da caccakar Shugaba Tinubu

Sunaye da bayanin sanatocin da suka taba gamuwa da matsala saboda sun kalubalanci shugaban kasa
Sanata Ali Ndume da Sanata Adolphus Wabara sun gamu da matsala bayan kalubalantar shugaban kasa. Hoto: @Waspapping
Asali: Twitter

Sanata Ali Ndume, mai wakiltar Borno ta Kudu da kuma tsohon Sanata Adolphus Wabara mai wakiltar Abia ta Kudu na daga cikin ‘yan tsirarun da suka fuskanci wannan matsalar, inji rahoton Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matsalolin da Sanata Ndume ya fuskanta

Mun ruwaito cewa an cire Sanata Mohammed Ali Ndume, daga mukamin bulalar majalisar dattawa bayan korafin da ya yi kan gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

A ranar 17 ga watan Yulin 2024 Sanata Ali Ndume ya kalubalanci gwamnatin APC a matakin kasa kan halin da talaka ke ciki, inda ya yi ikirarin cewa Shugaba Tinubu na wahalar gani.

Sai dai, ko a watan Janairun 2017, an taba cire Sanata Ndume daga matsayin jagoran majalisar dattawa ta 8 kan kalaman da ya yiwa shugaban majalisar na lokacin, Bukola Saraki.

Kara karanta wannan

Sanata Ndume ya maida martani ga Ganduje, ya faɗi yadda Buhari da Tinubu suka jawo shi APC

Bayan watanni biyu, a watan Maris din 2017, majalisar dattawa ta dakatar da Sanata Ndume na tsawon watanni shida, biyo bayan shawarar da kwamitinta mai kula da da’a ya bayar.

Kwamitin ya ba da shawarar dakatar da S|anata Ndume saboda ya furta wasu kalamai da suka taba martaba da da'ar majalisar dattawan.

Sanata Adolphus Wabara ya fuskanci matsaloli

Shi ma tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Wabara ya taba fuskantar matsala a lokacin da ya nuna adawa da shugaban kasa na lokacin, Olusegun Obasanjo.

An ce an fara takun saka tsakanin Obasanjo da Wabara ne lokacin da sanatan ya yi wani taron sanatocin Kudu maso Gabas a Ohambele da ke jihar Abi a Fabrairun 2005.

A lokacin, an ce sanatocin sun amince cewa shi kadai ne zai iya fitowa takarar shugaban kasa daga shiyyar a 2007, lokacin Obasanjo na neman tazarce karo na uku.

Jin cewa Sanata Wabara ya fara shirin adawa da takararsa, an ce Obasanjo ya yi jawabin kai tsaye a gidan talabijin, inda ya zargi sanatan da hannu a badakalar N55m na kasafin ilimi.

Kara karanta wannan

Kalamai a kan gwamnatin da suka tsumbula Sanata Ndume cikin ruwan zafi a APC da majalisa

A baya bayan nan, Sanata Wabara a wata hira da aka yi da shi ya yi ikirarin cewa ya ki karbar tayin N250m domin yarda da yunkurin Obasanjo na yin tazarce karo na uku.

Sanata Ndume ya kara sukar Tinubu

A wani labarin, mun ruwaito cewa Sanata Ali Ndume, wanda aka tsige daga muƙamin bulaliyar majalisar dattawa, ya ci gaba da caccakar gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Ndume ya ce sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000 da Shugaba Tinubu ya sanar ya yi kaɗan idan aka kwatanta da irin wahalar da ƴan Najeriya ke ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.