Jerin Sanatocin da suka tsige Ali Ndume

Jerin Sanatocin da suka tsige Ali Ndume

– Sanatocin APC sun tsige Ali Ndume daga Shugaban masu rinjaye a Majalisa

– Sanatoci 39 na APC cikin 63 suka sa hannu wajen tubbuke Ndume

– ‘Yan Majalisar Dattawa karkashin APC sun nemi Mataimakin Shugaba Ike Ekweremadu ya dawo Jam’iyyar su ta APC ko shima su tsige sa

Jerin Sanatocin da suka tsige Ali Ndume
Jerin Sanatocin da suka tsige Ali Ndume

Sanatoci 39 cikin 63 na Jam’iyyar APC da ake da su a Majalisar Dattawa suka saka hannu wajen tsige Ali Ndume daga kujerar sa. Tuni kuwa dai har an nada Sanata Ahmed Lawan a matsayin wanda zai maye gurbin na sa.

A wani kudirin da ke nuna rashin amanna da Sanata Ndume, Shugaban Majalisar Dattawar, Bukola Saraki, ya karanta takardar da ‘Ya yan APC suka aiko na cewa sun cire Ndume. Sai dai tuni ya wanke kan sa, yace ba shi ya kashe zomon ba, rataya kurum aka ba shi.

KU KARANTA: An damke wani babban dan ta'adda

Sanatocin da suka cire Ndume dai sun hada da: Dino Melaye, Sulaiman Nazif, Mustafa Bukar, Barau Jibrin, Rabiu Kwankwaso, Usman Nafada, Baba Garbai, Kabir Marafa,Tijjani Kaura, Sulaiman Hunkunyi, Shehu Sani, Ubale Shitu, Aliyu Abdullahi, Umaru Kurfi, Abubakar Yusuf, Kabir Gaya, Shaba Lafiagi, Ibrahim Gobir, Isa Misau.

Saura sun hada da Ali Wakili, Ahmed Bakura, Ahmed Lawan, David Ummaru, Danjuma Goje, Binta Masi Garba dsr.

Domin karin bayan a biyo mu a shafin mu na https://twitter.com/naijcomhausa da kuma https://www.facebook.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel