Wani kwamitin je-ka-nayi-ka ta dakatar da ni daga Majalisar Dattawa - Sanatan APC
Wani dan majalisar dokokin kasar, Sanata Ali Ndume, yace kwamitin majalisar dattawa da suka dakatar da shi a ranar 29 ga watan Mars sun kasance kwamitin je-ka-nayi-ka wanda shugaban majalisar masu rinjaye ke wakilta.
Ndume, wanda ke wakiltan Borno ta Kudu a majalisar dattawa, ya bayyana hakan ga kamanin dillancin labaran Najeria a Abuja a ranar Talata.
A cewarsa, kwamitin da ta bukaci a dakatar da ni, kwamiti ne da ke ingiza irin wannan lamari.
An dakatar da Ndume ne akan korafinsa na kira ga a binciki zargin da ake yi akan kammala jami’ar Ahmadu Bello na Sanata Dino Melaye.
Dakatarwan ya biyo bayan shawarwarin da kwamitin majalisada tayi bincike a zargin.
A baya Legit.ng ta rahoto cewa, kakakin majalisar wakilai, Mista Yakubu Dogara, ya bayyana cewa tarihi zai bayar da mumunan labari akan gwamnati mai mulki idan hart a gaza dakatar da yawan kashe-kashen bayin Allah da ake yi.
KU KARANTA KUMA: Fayemi ya gana da Buhari a fadar shugaban kasa
Dogara ya bayyana hakan a ranar Talata yayinda yake yiwa mambobin majalisar maraba da dawowa daga hutun karamar sallah.
Ya bayyana cewa ya zama dole a gaggauta dakatar da kashe-kashen bayin Allah da ake yi.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng