“Farar Ƙafa”: Ƙungiyar KYC Ta Faɗi Abin da Ya Jawo Gobara a Fadar Sarkin Kano Sanusi II
- Wata kungiyar matasan Kano (KYC) ta ce gobarar da ta tashi a fadar Sarkin Kano alama ce ta Allah na fushi da sake nadin Muhammadu Sanusi II
- Kungiyar ta yi ikirarin cewa sake nadin Sanusi II ya sabawa ka'ida, tare da yin kira gare shi da ya fice daga fadar domin gujewa wasu masifun
- Kungiyar KYC ta bukaci gwamnatin jihar da ta daina goyon bayan dawo da Sarki Sanusi, tare da mutunta doka, tana mai barazanar daukar mataki
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - Gamayyar kungiyoyin matasan Kano (KYC) ta danganta tashin gobarar da ta faru a fadar Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II da 'farar kafar sarkin.'
A cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar, Kwamared Abdullahi Nuhu ya fitar, kungiyar ta ce lamarin ya nuna karara cewa Allah ya yi fushi da sake nadin sarkin.
"Kotu ba ta amince da nadin Sanusi ba" - KYC
Jaridar Daily Trust ta ruwaito Nuhu ya ce kotu, al’ummarsa da kuma ubangiji ne suka ki amincewa da mayar da Sanusi II kan mukami.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta kara da cewa:
"Ci gaba da zama kan karagar Sarkin Kano da Muhammadu Sanusi II ya yi ya sabawa shari'a, kuma hakan ya nuna ba ya mutunta doka."
“Duk da hukuncin da kotu ta yanke na dakatar da rusa masarautun Kano, gwamnatin jihar na ci gaba da ba da kariya kan dawo da shi da ta yi."
Kungiya ta nemi Sanusi II ya bar fadar Kano
Kungiyar KYC ta bukaci Sarki Sanusi II da ya fice daga fadar ba tare da bata lokaci ba domin gujewa afkuwar wasu munanan lamura a gaba, inji rahoton jaridar The Nation.
Kungiyar ta yi ikirarin cewa ci gaba da zaman Sanusi II matsayin sarki barazana ce ga zaman lafiya da kwanciyar hankalin al'ummar jihar Kano.
“Muna kuma kira ga gwamnatin jihar da ta daina goyon bayan wannan haramtacciyar doka da kuma mutunta umarnin da kotu ta yi kan rusa nadin Sanusi II.
“Ba za mu zura idanuwa mu yi shiru ba yayin da ake karya doka kuma a ce za a hana mutanen Kano neman adalci. Muna kira da a sauke Sarki Sanusi II daga karagar mulki."
- A cewar sanarwar.
"Dalilin sake nadin Sanusi II" – Kwankwaso
A wani labarin kuma, mun ruwaito cewa dan takarar shugaban kasa na NNPP, Rabiu Kwankwaso, ya ce an mayar da Sanusi a matsayin Sarkin Kano domin cika alkawuran yakin neman zabe.
Kwankwaso ya ce Gwamna Kabir Abba Yusuf ya yi alkawarin mayarwa Sanusi II sarautar Kano idan aka zabe shi a matsayin gwamna a yakin neman zaben 2023.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng