Kamar Al’amara: Yadda Barawo Ya Yaudari Direban Kabu-Kabu da Farfesa, Ya Sace Motarsa

Kamar Al’amara: Yadda Barawo Ya Yaudari Direban Kabu-Kabu da Farfesa, Ya Sace Motarsa

  • Rahoton da muke samu ya bayyana yadda wani barawon mota ya yiwa direban Uber wayau tare da kwace masa mota
  • ‘Yan sanda sun yi nasarar kame bata-garin da ake zargin ya yi awon gaba da motar mutumin da ya yarda dashi
  • A Najeriya, sace mota ya zama ruwan dare, lamarin da ke kara sanya ‘yan kasar cikin rudani da tashin hankalin rashin aminci

Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

Jihar Legas - Rundunar 'yan sandan Jihar Legas, ta ce ta kama wani mutum da ake zargin ya sace motar kabu-kabu ta Uber bayan ya yaudari direbanta da faranti farfesu.

Mai magana da yawun rundunar, SP Benjamin Hundeyin ne ya tabbatar wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) aukuwar lamarin a ranar Asabar, Daily Nigerian ta tattaro.

Kara karanta wannan

Harka ta lalace: Mai aukuwa ta auku, an ba 'yan kasar waje wa'adin barin Sudan cikin gaggawa

An sace motar dan Uber daga siya masa farfesu
Daga siya masa farfesu, an sace motar dan Uber | Hoto: Wolfram Steinberg, Craig F. Walker/The Boston Globe
Asali: Getty Images

Yadda aka saci motar dan kabu-kabun Uber

Hundeyin ya ce Ofishin 'Yan Sanda na Akinpelu ya karbi rahoton koke a ranar 5 ga Yuli, da misalin karfe 8:00 na dare daga wani direban Uber, wanda ba a ambaci sunansa ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Direban ya ba da rahoton cewa ya dauki wani fasinja, wanda ya bayyana kansa da sunan Ishaya, daga tashar man NNPC da ke Maryland, a cikin motarsa kirar Toyota Corolla zuwa wani otal a yankin Oshodi.

Mai magana da yawun ‘yan sandan ya bayyana cewa, yayin da suke cikin otal din, wanda ake zargin ya siyawa direban abinci, farantin farfesu da kuma lemon kara kuzari guda daya.

Yadda ‘yan sanda suka kama barawon mota

Da yake jawabi, ya ce:

"Ana cikin haka, sai wanda ake zargin yake nemi audugar tsagule kunne, direban ya bashi makullin motarsa ya yi amfani da shi.

Kara karanta wannan

Ana dab da zabe: An harbi tsohon shugaban kasar Amurka Donald Trump a wani taro a Pennsylvania

"Direban ya kara da cewa wanda ake zargin ya sauka kasa bayan ya karbi makullin motar kana ya tafi da motarsa.
"Sai dai, wata tawagar 'yan sanda da ke aikin bincike a kan titin Boladale, sun yi nasarar cafke shi.
"Sadda ya gaza ba da cikakken bayanin takardun mallakar motar, sai kawai aka kama shi."

Ana ci gaba da bincike kan barawon mota

Hundeyin ya kara da cewa yayin da 'yan sandan suke shirin kai wanda ake zargin zuwa ofishin 'yan sanda, a nan ne direban ya zo wurin sannan ya ga motarsa.

Ya ce an tsare wanda ake zargin don ci gaba da bincike kafin daga bisani doka ta yi aiki a kansa daidai da laifinsa.

Ya zama ruwan dare a sace mota ko wata kadara ta mutum, lamarin da yak e kara sanya ‘yan kasar cikin damuwa.

An kama yara da kitsa sace mota

Kara karanta wannan

Allah mai yadda ya so: Bidiyon haduwar Umar Bush da Dangote a Villa ya girgiza jama'a

A wani labarin, rundunar ‘yan sandan jihar Enugu a Kudu maso Gabashin Najeriya ta ce ta kama wasu yara maza biyu da ake zargi da laifin fashi da makami a jihar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Daniel Ndukwe ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a daren Juma’a 17 ga watan Mayu.

Kakakin ya bayyana wadanda ake zargin da sunan Favor Akabue mai shekaru 18 da kuma Chiemezie Obayi mai shekaru 19 – dukkansu mazauna yankin Trans Ekulu a karamar hukumar Enugu ta Gabas a jihar, Premium Times ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.