Sarkin Ilemona: Dogarin Shugaba Bola Tinubu Ya Samu Babbar Sarauta a Jihar Kwara

Sarkin Ilemona: Dogarin Shugaba Bola Tinubu Ya Samu Babbar Sarauta a Jihar Kwara

  • Laftanal kanal Nurudeen Alowonle, dogarin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya zama sabon Sarkin Ilemona a jihar Kwara
  • Duk da masu nadin sarkin garin basu sanar a hukumance ba, wata majiya wacce jagora ce a yankin ta tabbatar da hakan
  • Ana sa ran Laftanal Yusuf zai yi amfani da gogewarsa wajen kawo ci gaba a yankin tare da dasawa daga inda magabatansa suka tsaya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kwara - An nada dogarin shugaban kasa Bola Tinubu, Laftanal kanal Nurudeen Alowonle Yusuf a matsayin sabon Sarkin Ilemona, hedikwatar karamar hukumar Oyun a jihar Kwara.

Duk da masu nada sarkin basu sanar da hakan ba a hukumance, wani fitaccen shugaban al'ummar yankin wanda ya bukaci a boye sunansa, ya tabbatar da nadin.

Kara karanta wannan

Cikakkun sunaye da bayanan jihohi 7 da ake son kirkira a Najeriya

Laftanal Kanar Nurudeen Yusuf, dogarin Shugaba Tinubu ya zama sarkin Ilemona da ke jihar Kwara.
Sarkin Ilemona: Dogarin shugaba Bola Tinubu ya sarauta a jihar Kwara. Hoto: @DejiAdesogan
Asali: Twitter

Majiyar ta ce tuni aka fara shirye-shiryen nadin dogarin shugaban kasan a matsayin sabon Sarkin Ilemona, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Zai kawo cigaba a yankin" - Majiya

Laftanal kanal Yusuf ɗa ne ga marigayi tsohon basarake, Oba Yusuf Omokanye Oyekanmi, Elemona na kasar Ilemona.

"Ana sa ranYusuf a matsayin sarkin Ilemona zai yi amfani da gogewarsa wurin gudanar da sha'anin mulkin masarautar tare da tabbatar da cigaba da hadin kai.
“A matsayin sabon sarki, Laftanal Kanal Yusuf zai kula da lamurran sarakunan gargajiya na garin Ilemona, sannan ya dora daga inda magabatansa suka tsaya.

- A cewar majiyar.

Gogewar Laftanal kanal Yusuf

Kamar yadda Tribune ta bayyana, bayan kammala karatunsa na difuloma a 2000, Nurudeen Yusuf ya shiga makarantar horar da hafsoshin soji dake Kaduna.

Tsakanin 2004 zuwa 2005, ya halarci makarantar sojoji ta Royal Sandhurst (RMAS) dake Ingila. A 2006, ya halarci makarantar horar da aikin sirri na rundunar sojin kasan Najeriya dake Legas.

Kara karanta wannan

"Hakurin talaka ya fara karewa": Sanatoci sun ankarar da Tinubu kan yunwa a kasa

A 2007, ya yi karatun horar da matasan hafsoshin sojoji a Kaduna inda ya samu gogewa kan amfani da makamai daban-daban domin ayyuka na musamman.

Dogarin Shugaba Tinubu ya kama aiki

A wani labarin, mun ruwaito cewa Laftanar Kanar Nurudeen Alowonle Yusuf, ya kama aiki a matsayin sabon mai tsaron lafiyar zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

A ranar Litinin, 1 ga watan Mayu, muka ruwaito cewa Yusuf ya kama sabon aikinsa mako uku kafin bikin rantsar da Shugaba Tinubu, bayan lashe zabe karkashin jam'iyyar APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.