Dogarin Shugaba Muhammadu Buhari, YM Dodo, ya samu karin girma zuwa Kanal, Hotuna

Dogarin Shugaba Muhammadu Buhari, YM Dodo, ya samu karin girma zuwa Kanal, Hotuna

  • Shugaba Buhari ya zauna da manyan hafsoshin tsaron tarayya yau a taron majalisar tsaro
  • Wannan ya biyo bayan kwana hudu jere ana garkuwa da matafiya a hanyar Kaduna zuwa Abuja
  • A zaman, Buhari tare da mataimakinsa sun kwalliya dogarinsa Kanal YM Dodo

FCT Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Alhamis, 25 ga Nuwamba, 2021 ya jagoranci zaman majalisar tsaro a fadar shugaban kasa, Aso Villa, Abuja.

Gabanin fara taron zaman tsaron, Shugaban kasan ya kwalliye dogarinsa, YM Dodo, wanda ya samu karin girma daga Laftanan Kanal zuwa Kanal a hukumar Soji.

Hadimin Shugaban kasa, Buhari Sallau, ya bayyana hakan a shafinsa na Faebook.

Wadanda ke hallare lokacin wannan taro sun hada da Mataimakin Shugaban kasa, Yemi Osinbajo; matar YM Dodo, Shugaban hukumar NIA, Amb Rufai; da NSA Babagana Munguno.

Read also

Labari cikin Hotuna: Shugaba Buhari na jagorantar taron majalisar zartarwa FEC a Aso Villa

Dogarin Shugaba Muhammadu Buhari, YM Dodo
Dogarin Shugaba Muhammadu Buhari, YM Dodo, ya samu karin girma zuwa Kanar, Hotuna Hoto: Buhari Sallau
Source: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hakazalika Shugaban Hafsoshin tsaro, Janar Lucky Irabor; babban hafsan Sojin sama, Air Marshal Amao; Babban Hafsan Sojin kasa, Laftanar Janar Faruq; da Hafsan Sojin Ruwa, Rear Admiral AS Gambo.

Dogarin Shugaba Muhammadu Buhari
Dogarin Shugaba Muhammadu Buhari, YM Dodo, ya samu karin girma zuwa Kanar, Hotuna Hoto: Buhari Sallau
Source: Facebook

Dogarin Shugaba Muhammadu Buhari, YM Dodo, ya samu karin girma zuwa Kanar, Hotuna
Dogarin Shugaba Muhammadu Buhari, YM Dodo, ya samu karin girma zuwa Kanar, Hotuna Hoto: Buhari Sallau
Source: Facebook

Source: Legit.ng

Online view pixel