Sabbin hafsoshin sojoji sun isa Maiduguri don magance rashin tsaro
- Sabbin hafsoshin sojojin da shugaba Muhammadu Buhari ya nada sun isa jihar Borno a ranar Lahadi
- An bayyana cewa hafsoshin sun isa garin Maiduguri domin zaman tattauna yadda zasu bullowa ta'addanci a yankin
- Hafsoshin zasu kuma zauna da masu ruwa da tsaki a yankin don tabbatar da tsaro da zaman lafiya
Sabbin hafsoshin sojan Najeriya sun isa Maiduguri, babban birnin jihar Borno tare da niyyar ganawa da masu ruwa da tsaki don shawo kan yadda za a magance tayar da kayar baya a fagen daga.
Babban hafsan hafsoshin tsaro, Manjo Janar Leo Irabor ya jagoranci shugabannin hafsoshin zuwa hedikwatar rundunar tsaro ta rundunar Operation Lafiya Dole da ke Maiduguri da misalin karfe 1:30 na rana a ranar Lahadi.
Wata babbar majiyar tsaro da ta bayyana wa wakilin Daily Trust ta bayyana cewa shugabannin rundunonin tare da sauran masu ruwa da tsaki ana sa ran za su yi tunani da sake dabarun yadda za su bullo da wata hanyar da za ta tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a yankin.
KU KARANTA: Wani dan majalisa ya harbe wanda ake zargin dan fashi da makami ne
Daily Trust ta ruwaito cewa dukkanin shugabannin hafsoshin da aka nada kwanan nan sun halarci taron.
Ciki har da Shugaban hafsan hafsoshin tsaro, Manjo Janar Leo Irabor; Shugaban hafsan soji, Manjo Janar Ibrahim Attahiru; Shugaban hafsan sojin ruwa, Rear Admiral Awwal Gambo da shugaban hafsan sojin sama, Air Vice Marshal Isiaka Amao duk sun halarci taron.
KU KARANTA: Gwamnan jihar Borno Babagana Zulum ya nada sabon Shehun Dikwa
A wani labarin, Wata kungiya, Arewa Youth Initiative for Peace and Good Leadership, ta yi kira ga sabbin shugabannin rundunonin da aka nada da su nuna kishin kasa da cikakkiyar gaskiya wajen gudanar da ayyukansu, The Nation ta ruwaito.
Matasan, wadanda suka yi magana ta bakin Shugabansu, Mohammed Rilwanu, a cikin wata sanarwa, sun yaba wa Shugaba Muhammadu Buhari saboda sauraren muryar mutane ta hanyar sallamar tsoffin shugabannin rundunonin.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng