Wayas: Gawar Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa da Ya Mutu a Landan Ta Iso Najeriya

Wayas: Gawar Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa da Ya Mutu a Landan Ta Iso Najeriya

  • Kimanin shekaru biyu da watanni tara bayan rasuwarsa, gawar tsohon shugaban majalisar dattawa, Joseph Wayas, ta isa Najeriya
  • Mista Wayas dai ya rike mukamin shugaban majalisar dattawa daga Oktobar 1979 zuwa Disambar 1983, kuma ya rasu ne a birnin Landan
  • A lokacin wallafa wannan rahoto, an dauki gawar marigayin daga filin jirgi zuwa babban asibitin kasa da ke Abuja, domin shirin binne shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Gawar marigayi tsohon shugaban majalisar dattawa, Joseph Wayas, ta iso Najeriya bayan kimanin watanni 33 da mutuwarsa a wani asibitin Landan a Nuwamban 2021.

Mista Wayas, ya kasance shugaban majalisar dattawa tsakanin 1 ga Oktobar 1979 zuwa 31 ga Disambar 1983, kuma ya rasu yana da shekara 80 bayan ya yi fama da rashin lafiya.

Kara karanta wannan

Najeriya za ta samu bashin $150bn da halatta auren jinsi a yarjejeniyar Samoa?

An iso da gawar Joseph Wayas Najeriya bayan watanni 33 da mutuwarsa a Landan
Joseph Wayas: Gawar tsohon shugaban majalisar dattawa ta iso Najeriya. Hoto: @ChidiOdinkalu
Asali: Twitter

Gawar Joseph Wayas ta iso Najeriya

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa an doro gawar Joseph Wayas ne kan jirgin British Airways 083 daga Landan, kuma ya ta iso Abuja misalin karfe $:40 na Asubah.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ce ita ma matarsa ​​ta rasu bayan kwanaki 12 da mutuwarsa amma an binne ta, sai ita gawar dan siyasar ce aka ajiye a dakin ajiye gawa na Landan, lamarin da ya jawo cece kuce.

Jarigbe Agom, Peter Akpanke, ‘yan uwa da sauran masu ruwa da tsaki daga ahalin Joseph Wayas ne suka tarbi gawar ta tare da ajiye ta a dakin ajiye gawa na babban asibitin kasa dake Abuja.

Manyan baki sun fara zuwa ta'aziyya

Da yake zantawa da manema labarai, Sanata Jarigbe ya gode wa gwamnan jihar Cross River, Bassey Otu bisa yadda ya taimaka wajen dawo da gawar Joseph Wayas daga Landan.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi garkuwa da tsohon shugaban kungiyar NLC, an samu bayanai

Sanata Jarigbe Agom, mai wakiltar Cross River ta Arewa ya ce yana da yakinin cewa Gwamna Otu zai shirya gagarumin bikin binne tsohon shugaban majalisar, in ji rahoton Vanguard.

Tun bayan isowar gawar ne aka ruwaito cewa manyan baki na ci gaba da sanya hannu kan littafin ta’aziyyar marigayin a gidan sa na Asokoro da ke Abuja.

Akwai tarin bindigogi a majalisar dattawa

A wani labarin, mun ruwaito cewa sanata mai wakiltar Ondo ta Kudu, Jimoh Ibrahim, ya ce yana da manhaja a wayarsa da ke gano adadin bindigogin da suke kewaye da shi.

Sanatan ya yi ikirarin cewa a dai dai lokacin da ya ke wannan maganar, manhajar ta nuna masa cewa akwai akalla bindigogi 277 a cikin ginin majalisar dattawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.