EndSARS: Kotun ECOWAS Ta Dauki Mataki Kan Gwamnatin Najeriya, Ta Gindaya Sharuda
- Yayin da ake zargin Gwamnatin Tarayya da take hakkin dan Adam a zanga-zangar EndSARS, kotun kungiyar ECOWAS ta gano laifuffukan gwamnati
- Kotun ta bayyana cewa gwamnatin ta ci zarafi tare da take hakkin masu zanga-zangar EndSARS da aka yi a shekarar 2020
- Kotun ta umarci gwamnatin ta biya kowa daga cikin wadanda suka shigar da korafin N2m a matsayin diyyar take musu hakki
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Kotun kungiyar ECOWAS ta bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta take hakkin dan Adam a zanga-zangar EndSARS.
Kotun ta ce gwamnatin ta ci zarafin Obianuju Catherine Udeh da wasu mutane biyu yayin zanga-zangar a shekarar 2020.
EndSARS: ECOWAS ta gano matsaloli a zanga-zangar
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kotun ta fitar bayan zamanta a yau Laraba 10 ga watan Yulin 2024, cewar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Har ila yau, kotun ta samu Gwamnatin Najeriya da saba dokar kare hakkin dan Adam ta African Charter sashe na 1, 4, 6, 9 da kuma 10.
Ta ce Gwamnatin ta take hakkin masu zanga-zangar musamman abin da ya shafi 'yancin fadar baki da taro da kuma basu tsaro, Vanguard ta tattaro.
Kotun ta umarci gwamnatin ta biya diyya
Kotun daga bisani, ta umarci gwamnatin ta biya kowane daga cikin masu korafin N2m a matsayin diyyar take musu hakki.
Wadanda suka shigar da korafin sun hada da Obianuju Udeh da Perpetual Kamsi da Dabiraoluwa Adeyinka.
Masu korafin suna zargin take musu hakkinsu na 'yan Adam a zanga-zangar lumana a aka gudanar a watan Oktoban 2020 a jihar Lagos.
Kotu ta shirya hukunci kan karar Tinubu
Kun ji cewa Kotun Koli ta shirya dauar mataki kan korafin da Bola Tinubu ya shigar da gwamnonin jihohin Najeriya.
Shugaban ya shigar da korafin ne kan yadda gwamnonin ke tafiyar da kananan hukumomi ta hanyar da bai dace ba.
Rahotanni sun tabbatar da cewa Kotun Ƙolin za ta yanke hukunci kan ƙarar a gobe Alhamis, 11 ga watan Yulin 2024.
Asali: Legit.ng