EndSARS: Gwamnatin Legas ta gayyace mu - Rundunar Sojojin Najeriya

EndSARS: Gwamnatin Legas ta gayyace mu - Rundunar Sojojin Najeriya

- Lamarin ya yi ƙamarin daya tilastawa gwamnati amfani da sojoji don kwantar da tarzoma

- Bidiyon da ke yawo a kafafen sadarwa aiki ne na masu ƙage da ke son ganin bayan rundunar soji

- Rundunar soja ta ce bata harbi ko mutum daya ba a abin da ya faru a Lekki

Runduna ta 81 ta sojojin Najeriya ta magantu akan shirun da ta yi dangane da harbe-harben Lekki Toll Gate, Legas, inda ta ta ce an kai sojojin ne bisa umarnin gwamnatin jihar.

Daily Trust ta tattaro bayanan daga masu zanga-zangar wai an harbe su a yunƙurin tarwatsa su da sojojin da aka kawo suke yi daga gudanar da zanga-zanga wadda dubban matasa suka fito don nuna ƙin amincewarsu da zalunci da tozarcin rundunar SARS.

Hukumomin da suke kula da rundunar 81 sun bayyana ce an kawo sojojin bisa umarnin gwamnatin jihar Legas don ganin dokar ta ɓacin da aka sanya ta fara aiki a ranar Larabar makon da ya gabata.

EndSARS: Gwamnatin Legas ta gayyace mu - Rundunar Sojojin Najeriya
EndSARS: Gwamnatin Legas ta gayyace mu - Rundunar Sojojin Najeriya. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

A wani jawabi da rundunar 81 ta sojin Najeriya wadda ta samu sa hannun jami'in hulɗa da jama'a na rundunar Manjo Osoba Olaniyi, yace iƙirarin da ake yi na sun aikita kisan kiyashi ba gaskiya bane kuma bashi da makama ballantana tushe.

KU KARANTA: Mutum 13 ne suka rasu a hadarin mota a babban titin Kano zuwa Kaduna

A wata sanarwa da rundunar ta fitar mai taken "Iƙirarin kashe masu zanga-zangar EndSARS a Lekki toll gate," Hankalin rundunar mu ya kai kan wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sadarwar zamani wanda ke nuni da kashe fararen hula masu zanga-zanga da sojoji suka yi a Lekki Tollgate Plaza.

"Wannan iƙirarin ba gaskiya bane, bashi da tushe kuma an ƙirƙireshi don kawo tashin hankali da hargitsi a ƙasa.

Babu lokacin da sojoji suka taɓa buɗewa wani farar hula wuta, a cewarsa.

Daga fara zanga-zangar EndSARS babu wani jami'in rundunar 81 da ya taɓa sa hannunsa cikin lamurran zanga-zangar.

DUBA WANNAN: Abin da yasa muka jinkirta rabon tallafin korona a Sokoto - Gwamna Tambuwal

"Sai dai kuma duk da cewa, gwamnatin Legas ce ta ɗauki matakin yin amfani da sojoji bayan ta saka dokar ta baci na awa ashirin da hudu.

"Hakan ya faru ne saboda tashin hankalin da ya janyo ƙona ofisoshin 'yan sanda da dama, kashe 'yan sanda, sakin wanda ke tsare a hannun su da kuma sace makamai.

"Lamarin ya yi ƙamari kwarai. A wannan hali ne gwamnati ta ga bata da wata mafita face ta nemi shigowar sojoji cikin lamarin don kwantar da tarzoma.

"Shigowar sojoji cikin lamarin ya biyo bayan tsare tsare da akayi na jami'an tsaron cikin gida da kuma sojoji da aka hada rundunar hadin gwiwa wanda yana kunshe cikin dokar aikin hadin gwiwa (ROE) na aikin cikin gida.

Daga karshe, hedikwatar soji ta 81 a kokarin tabbatar da bin doka bata harbi wani mutum ba, kuma akwai hujjoji gamsassu akan hakan.

"Wannan ƙage ne na masu son bata sunan sojojin Najeriya wanda bazai tsinana musu komai ba.

Muna kira ga al'umma da suyi watsi da ƙagen saboda babu kanshin gaskiya a cikinsa," a cewarsa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel