EndSARS: Buhari ya aike wa matasa muhimmin sako ta hannun Gambari da sarakuna

EndSARS: Buhari ya aike wa matasa muhimmin sako ta hannun Gambari da sarakuna

- Shugaba Buhari ya ce shugaban ma'aikatansa, Farfesa Gambari, zai raka manyan ma'aikatan gwamnati wurare da ke kasar nan

- Ya roki shugabannin gargajiya da sanar da matasa cewa ya ji kukansu kuma zai share hawayensu, su kwantar da hankalinsu

- Ya kara da bayyana musu cewa su kadai ne suka san yadda za su fahimtar da matasan, don su iyaye ne ga al'umma

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce shugaban ma'aikatansa, Farfesa Ibrahim Gambari, zai jagoranci manyan ma'aikatan gwamnati zuwa wurare daban-daban a cikin kasa a matsayin daya daga cikin ayyukan da matasa suka bukaci a yi.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tattauna da shugabannin gargajiya a kan matsalolin da Najeriya take fama da su, daga Daily Nigerian.

Ya rokesu da su taimaki mulkinsa wurin kwantar da tarzoma musamman wacce matasa suka tayar, a sanar da matasa cewa ya ji kukansu kuma yanzu haka yana iyakar kokarinsa wurin ganin ya daidaita al'amura.

Kamar yadda takardar da mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman a kan labarai ya saki, Femi Adesina, shugaban kasa ya fadi hakan yayin da ya ke yi wa shugabannin gargajiya bayani, wanda sarkin Sokoto ya jagoranta a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

KU KARANTA: Za a raba kyautar mita sama da miliyan 1 ta wutar lantarki - Buhari

Takardar mai taken, "shugaban kasa ya bukaci shugabannin gargajiya su tattauna da matasa."

Adesina ya yanki daidai yadda shugaban kasa yayi ta maimaita bukatar goyon bayan shugabannin gargajiya a kan tattaunawa ga matasa.

"Mun ji kukan matasa da yaranmu, kuma muna nan muna aikin a kan gyara matsalar.

"Don cin nasara a kan wannan, muna bukatar goyon bayanku, ku kuma isar da sakonmu.

"Kun san yadda za ku tara mutanenku don tattaunawa dasu, ku tabbatar musu da cewa zamu share musu hawayensu," cewar Buhari, inji kakakinsa.

EndSARS: Buhari ya aike Gambari da wasu jiga-jigan makusantan shi jihohinsu
EndSARS: Buhari ya aike Gambari da wasu jiga-jigan makusantan shi jihohinsu. Hoto daga @daily_nigerian
Asali: Twitter

KU KARANTA: Matashi mai shekaru 29 ya bayyana yadda yayi noma shinkafa da rogo na N1m

A wani labari na daban, hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta sanar da lokacin da za ta cigaba da yin rijista ga masu (CVR) zabe, za su fara ne a watannin farko na 2021 saboda gabatowar zaben 2023.

An ware wa INEC naira biliyan 1 don yin CVR din, Channels Tv ta ruwaito. Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya sanar da hakan ranar Laraba lokacin da ya gabatar da kasafin INEC ga majalisar dattawa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel