Dalilin da ya sa NNPC za ta ci bashi domin samun kashi 20 a matatar man Dangote – Mele Kyari

Dalilin da ya sa NNPC za ta ci bashi domin samun kashi 20 a matatar man Dangote – Mele Kyari

  • Shugaban Kamfanin Man NNPC ya ce kamfanin ba zai zama dan kallo a harkar kasuwancin matatar man Dangoten ba
  • Ya ce harka ce da ke inganta tattalin arzikin kasa kuma mai dorewa
  • Sai dai ya ce ba da kudin gwamnati kamfanin zai sayi hannun jarin ba

Manajan Darakta na Kamfanin Man Fetur na Najeriya, (NNPC) Mele Kyari, a ranar Talata ya bayyana dalilin da ya sa kamfanin ke kokarin sayen kaso a matatar mai ta Dangote.

Ya yi bayanin haka a hirar da ya gabatar a tashar ChannelTV.

Ana sa ran matatar za ta fara aikin tace man a shekarar 2022 inda za tana tace ganga 650,000 a kowace rana.

Ana ganin matatar a matsayin gagaruma ta fuskar inganta makamashi a Najeriya da ma nahiyar Afirka baki daya.

A watan Mayu, kamfanin man NNPC ya bayyana cewa yana shirin mallakar kashi 20 na hannun jarin kamfani mai zaman kansa wanda hamshakin attajirin nan Aliko Dangote yake tafiyarwa.

"Babu wata kasa da ta dogara da albarkatu da za ta ci gaba da zura ido a harkar kasuwanci mai karfi irin wannan da ke da tasiri a sha’anin tattalin arzikin kasa, kuma a ce wai kasar ba ta da wani abin fada a ciki,"

kamar yadda Mista Kyari ya fada a ranar Talata a wani shirin kafar telebijin na Channels.

DUBA NAN: Ina PDP, ba zan yi butulci ba, ba zan koma APC ba: Mataimakin gwamnan Zamfara

Shugaban Mele Kyari
Dalilin da ya sa NNPC za ta ci bashi domin samun kashi 20 a matatar man Dangote – Mele Kyari Hoto: NNPC
Asali: Facebook

KU KARANTA: Wata mata tana neman mutumin da ta aura a dandalin taron dalibai tun lokacin suna firamare

Ya nuna cewa kamfanin ya yanke shawarar zuba jarin nasa ne lura da gwaggwabar ribar da ke tattare a harkar kasuwancin matatar man.

Ya kara da cewa:
"A sayan hannun jari a matatar man ta Dangote, ba wai kudin gwamnati za mu dauka domin sayan hannun jarin ba, wanda wannan shi ne kuskuren da mutane suke yi,"
“Rance za mu karbo domin shiga a dama da mu a wannan kasuwancin.
“Mun kwana da sanin cewa harkar matatar mai bullewa ce kuma tana da inganci, za ta aiki kuma za ta samar da riba. Za ta bayar da gudummawa ga tattalin arziki wanda zai zama dorewa saboda a cikin gajeren lokaci za ta ci gaba da kasancewa mai dorewa.
"Wannan ne dalilin da ya sa bankuna suke ba mu rance, don haka za mu iya sayan hannun jari a ciki.
"Sai dai wani gaskiyar lamarin kuma a nan shi ne ita ce idan ba ka yi hankali ba za ka iya azawa 'yan Najeriya wani farashin da ya zarce farashin da ya kamata su sayi man."

A halin yanzu dai kamfanin man NNPC shi ne kadai yake da wuka da nama da yake da dama a hukumance wajen shigo da man fetur cikin Najeriya.

Ba zamu kara farashin man fetur ba a watan Yuli, NNPC

Kamfanin man feturin Najeriya NNPC ya ce farashin litan man fetur zai cigaba da kasancewa N162 a watan Yulin da za'a shiga kuma ba za'a kara ba.

Shugaban kamfanin NNPC, Malam Mele Kyari, ya bayyana hakan ranar Talata.

Ya ce ana cigaba da tattaunawa da kungiyoyin kwadago kan farashin da ya kamata a sanya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel