“Hakurin Talaka Ya Fara Karewa”: Sanatoci Sun Ankarar da Tinubu Kan Yunwa a Kasa
- Majalisar dattawa ta nemi shugaban kasa Bola Tinubu da ya yi gaggawar nemo hanyoyin magance matsalar tsadar abinci
- Majalisar ta yi nuni da cewa yunwa da tsadar abinci sun addabi jama'a wanda har ta kai ga hakurin 'yan kasar ya fara karewa
- Sanatocin sun nuna damuwa kan yadda aka samu hauhawar farashin kayan masarufi zuwa kashi 40.66 a watan Mayun 2024
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Majalisar dattawa ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta magance matsalar yunwa da ake fama da ita a kasar sakamakon karancin abinci.
A cewar majalisar dattawan, ya zama wajibi gwamnatin Shugaban Bola Tinubu ta dauki matakan yaki da matsalar karancin abinci da ake fama da ita a kasar nan.
Sanatoci sun aika sakon gargadi ga gwamnati
Sanatocin sun yi gargadin cewa, sakamakon yunwa da talauci a cikin kasa, hakurin jama'a ya fara karewa, wanda ka iya kai ga tashin tashina, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majalisar dattijan ta yi nuni da cewa, a cikin ‘yan watannin nan an samu hauhawar farashin kayan masarufi, lamarin da ya haifar da tabarbarewar yanayin rayuwa na galibin ‘yan Najeriya.
A wani matakin gaggawa na magance matsalar abinci, majalisar dattawa ta bayyana cewa gwamnatin tarayya ta tura tireloli 60 na takin zamani a kowace jihar Najeriya.
Kudurin majalisar dattawa kan tsadar abinci
Matsayar majalisar dattawan jiya ya biyo bayan wani kudiri mai taken, “Bukatar gaggawa ta magance matsalar karancin abinci a Najeriya,” wanda Sanata Sunday Karimi da Sanata Ali Ndume suka gabatar.
Jaridar Tribune ta ruwaito Sanata Karimi ya ce:
“Rahoton da hukumar NBS ta fitar ya nuna cewa hauhawar farashin kayan abinci a kasar ya karu zuwa kashi 40.66 a Mayun 2024, wanda ya karu daga kashi 24.82 na watan Mayun 2023."
A nasa jawabin, Sanata Ndume wanda ya koka da cewa wannan shi ne karo na farko da aka sanya Najeriya cikin jerin kasashen da ke fama da matsalar karancin abinci, ya ce:
"Hukumar samar da abinci ta duniya ta ce sama da mutane 32m ne ake sa ran za su fuskanci matsalar yunwa a tsakanin watan Yuni da Agusta, wanda zan iya cewa mun fara ganin hakan."
NBS: Jerin jihohi mafi tsadar abinci
A wani labarin, mun ruwaito cewa hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta bayyana cewa hauhawar farashin kayan abinci a watan Janairun 2024 ya kai 35.41% bisa dari a ma’aunin shekara.
Hukumar ta kididdigar ta bayyana hakan ne a cikin rahoton farashin kayan masarufi da fitar na Janairun 2024 inda ta zayyana jihohin Najeriya mafi tsadar abinci.
Asali: Legit.ng