Rashin Aikin Yi: Ganduje Ya Ba Matasa Shawarar Abin da Za Su Yi Bayan Kammala Karatu
- Tsohon gwamnan Kano kuma shugaban jam'iyyar APC na kasa., Abdullahi Ganduje, ya ce tsarin ilimin Najeriya na da nakasu
- Abdullahi Ganduje ya shwarci matasa da su fantsama wurin koyon sana'o'in dogaro da kai domin magance rashin aikin yi
- Shugaban jam'iyyar ya jaddada cewa gwamnati ba za ta iya samarwa kowa aikin ba, don haka dole matasa su kirkiro aikin da kansu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Legas - Tsarin ilimin Najeriya ya samu caccaka inda shugaban jam'iyyar APC mai mulki, Abdullahi Ganduje ya ce shi ke kawo rashin aikin yi a kasar.
Abdullahi Ganduje ya bayyana hakan ne yayin da miliyoyin 'yan Najeriya ke fama da tsananin rashin aiki duk da da yawansu sun kammala karatu.
Kamar yadda ya ce, dalibai ba sa koyon dabarun sana'o'in dogaro da kai sakamakon nakasu da ke a tsarin karatun kasar, wanda ke haifar da rashin ayyukan yi, rahoton Vanguard ya bayyana.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Tsarin ilimin Najeriya ya gaza" - Ganduje
Ganduje ya yi jawabin ne a taron bude shirin horarwa na sana'o'in hannu domin matasa a Legas, wanda shugaban matasa na jam'iyyar APC na kasa, Dayo Israel ya shirya.
Tsohon gwamnan Kanon ya yarda cewa idan aka fara horar da matasa sana'o'i, Najeriya za ta samar da masu digirin da ba karatu kadai suka sani ba, har da kasuwanci da kirkire-kirkire.
An ce Ganduje ya samu wakilcin mataimakin shugaban jam'iyyar na Kudu, Cif Emma Eneukwu, kuma ya yi kira da ayi garambawul a fannin ilimi.
Ya jajanta yadda masu digiri a Najeriya suka kware a turanci amma babu aikin hannu, banda ire-irensu dake kasashen waje kama China da Indiya.
"Ba kowa zai samu aikin gwamnati ba" - Ganduje
Jaridar The Sun ta ruwaito shugaban APC din ya shawarci matasa da su canza lale tare da fifita koyon sana'a yayin da suke makaranta.
Ya bayyana cewa satifiket kadai ba zai isa ba, kuma ya shawarce su da suyi tunanin habaka sana'o'i sannan su zama 'yan kasuwa da al'umma za ta amafana da su.
Tsohon gwamnan Kanon ya jaddada cewa gwamnati ba za ta iya samarwa kowa aiki ba, don haka ya zama wajibi jama'a su kirkiri damarsu tare da bada gudumawa ga cigaban Najeriya.
Gwamna ya kori shugabannin makarantu 7
A wani labari na daban, Gwamnan jihar Taraba ya sanar da cewa ya kori wasu shugabannin makarantun sakandare har su bakwai a jiharsa.
Ma'aikatar ilimin jihar ce ta fitar da sanarwar korar shugabannin makarantar bayan da aka kama su da laifin karbar kudi daga hannun dalibai alhalin gwamnati ta hana.
Asali: Legit.ng