Yadda aikin Gwamnati ya zama na su wane-da-wane a mulkin Buhari

Yadda aikin Gwamnati ya zama na su wane-da-wane a mulkin Buhari

Mun samu labari daga Daily Trust cewa aiki a Gwamnatin Tarayya na nema ya zama kayan gabas inda sai su wane-da-wane su ke iya samu a wannan Gwamnati. ‘Yan Majalisu da manyan mukarabban Gwamnati ne ke yin yadda su ka so.

Yadda aikin Gwamnati ya zama na su wane-da-wane a mulkin Buhari
Aikin Gwamnati ya zama na yaran manya a Najeriya

A halin yanzu sai Talaka yayi da gaske zai iya samun aiki ganin yadda Minstoci da Sarakuna da sauran manya ke hana a dauki yaran Talakawa. A cikin shekaru uku na Gwamnatin APC dai da wuya ka ga ana tallar bada aiki a Ma’aikatun kasar.

Manyan Ma’aikatu irin su CBN, NNPC, NDIC, FIRS, PTAD, da sauran su duk su na daukar aiki ne a boye. Hukumar FCC da ya kamata ace tana tabbatar da adalci ba ta aikin ta. Ana raba aikin ne dai ga ‘Yan Majalisu da ‘Yan fadar Shugaban kasa.

KU KARANTA: Abin da ya sa za mu rabawa Talakawa kudin sata - Buhari

Rahotanni sun tabbatar da cewa Ma’aikatun Gwamnatin Tarayya 183 cikin 185 da ake da su sun dauki mutane 13, 780 aiki a cikin shekaru 2. Daga ciki dai mutum 6, 917 da aka dauka ba su bi wata ka’idar daukar aiki na kasar ba kamar yadda ya dace.

A kwanaki dai Daily Trust ta rahoto cewa babban bankin Kasar watau CBN ya dauki mutum fiye da 900 aiki a boye. Haka dai wasu da-dama su ke yi ba tare da tallatar da cewa ana neman ma’aikata a gidajen Jaridu ba. Talaka dai na ganin ta kan sa a halin yanzu.

Kwanaki kun ji cewa Sheikh Ahmad Gumi wanda fitaccen Malamin addinin Musulunci ne a kasar nan a wata doguwar hira da yayi da Jaridar nan ta Punch ya bayyana cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya raba kan Jama’ar Najeriya a mulkin sa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel