Gina Layin Dogo: Ana Fama da Matsin Tattali, Tinubu Zai Karbo Sabon Bashi Daga China
- Shugaban kasa Bola Tinubu ya ba mataimakinsa, Kashim Shettima umarnin ganawa da shugaban kasar Sin, Xi Jinping
- An ce Kashim Shettima zai tattauna da Shugaba Xi Jinping ne kan bukatar Najeriya na neman rancen kudi daga kasar Sin
- Kamar yadda ministan sufuri, Sanata Said Alkali ya bayyana, za ayi amfani da kudin ne wajen gina titutunan jirgin kasa a kasar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Gwamnatin Najeriya na shirin neman tallafin kudi daga gwamnatin kasar Sin domin gina titunan layin dogo daga Ibadan zuwa Abuja da Kaduna zuwa Kano.
Ministan sufuri, Sanata Said Alkali ne ya bayyana hakan yayin da kwamitin hadin gwiwa na majalisar tarayya kan sufuri ya kai ziyarar duba ayyukan layin dogo na Kaduna zuwa Kano.
Najeriya za ta karbo bashi daga Sin
Bisa umarnin Shugaba Bola Tinubu, ana sa ran mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima zai tattauna da shugaban kasar Sin, Xi Jinping domin samun kudaden, inji rahoton The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanata Alkali ya ce rashin kudi ya jawo cikas ga ga cigaban ayyukan layin dogon, yana mai cewa gwamnatin tarayya ta samu rancen kudin kammala titin layin dogon Kano zuwa Kaduna.
Ministan ya kuma yi ishara da cewa ma’aikatar ta hada kai da jami’an tsaro domin sanya ido tare da tabbatar da cewa ba a lalata kayayyakin aikin jiragen kasan ba.
Majalisa za ta duba batun karbo bashin
Jaridar The Guardian ta Shugaban kwamitin majalisar dattawa mai kula da harkokin sufurin kasa, Sanata Adamu Aliero ya yi Allah wadai da yadda bata gari ke sace kayan aikin gina titunan.
Sanata Aliero ya ce majalisar za ta tattauna da hukumar kula da basussuka ta kasa (DMO), ministan kudi, Antoni Janar na tarayya, da ministan sufuri domin ganin an karbo bashin.
Shugaban kwamitin ya ce karbo bashin tare da kammala ayyukan titunan zai bunkasa tattalin arziki, yayin da ya ce za a duba yiwuwar yin doka kan masu sace kayan aikin layukan dogon.
Bashin waje da ake bin Najeriya ya karu
A wani labarin, mun ruwaito cewa hukumar kula da basussuka ta kasa (DMO) ta sanar da cewa, adadin bashin da ake bin Najeriya ya zuwa watan Disamban 2023 ya kai $42.49bn.
Kamar yadda bayanan basussukan waje suka bayyana, Najeriya na cikin bashin China da wasu kasashen duniya dumu-dumu ciki har da Faransa, Indiya da Jamus
Asali: Legit.ng