Kowa Ya Yi Ta Kansa: Kura Ta Tsinke Daga Gidan Adana Namum Daji a Jos

Kowa Ya Yi Ta Kansa: Kura Ta Tsinke Daga Gidan Adana Namum Daji a Jos

  • Wata Kura ta tsere daga gidan adana namun daji da ke Jos, inda aka nemi jama'a su taimaka da bayanai domin kamo ta
  • Shugaban hukumar yawon bude idanu a jihar, Chuwanng Pwajok ne ya bayyana cewa Kurar ta gudu bayan an neme ta an rasa
  • Ya tabbatarwa da jama'a cewa kwararrun jami'ansu na kokarin bin sawunta ta hanyar amfani da jirgi mara matuki

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. Jihar Plateau- Hukumar kula da yawon bude idanu a jihar Filato ta bayyana cewa kura ta tsere daga gidan adana namun daji na Jos. Hukumar ta fitar da sanarwa dauke da sa hannun shugabanta, Chuwang Pwajok bayan an nemi kura an rasa a dakin da aka ajiye ta.

Kara karanta wannan

Auren jinsi: Yadda kururuwar mutanen Kano ya dakile yunkurin kungiyar LGBTQ

Hyena
Kura ta tsere a Jos Hoto: pjmalsbury
Asali: Getty Images

Jaridar Leadership ta wallafa cewa gidan adana namun daji na Jos na daya daga wuraren da aka tabbatar da adana yanayi mai kyau da namun dawa.

An nemi daukin jama'a don kamo Kura

Mahukunta a jihar Filato sun nemi daukin jama'a wajen bayar da bayanai kan kurar da ta tsere daga gidan adana namun dawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

The Guardian ta wallafa cewa kwararrun ma'aikatan gidan adana dabbobin na kokarin bin sawun kurar domin kamo ta cikin ruwan sanyi.

Haka kuma an baza jirgi marar matuki domin hasko kasa da zummar gano inda kurar ta shige.

Chuwang Pwajok ya ce duk wanda ya ganta ko ya samu wani bayani a kan kurar ya gaggauta tuntubar su.

Ya kara da bawa jama'a tabbacin cewa za a gaggauta gano kurar kafin ta yi barna cikin mutane.

An gano jarumar mace da Zalunta

Kara karanta wannan

NELFUND ta lissafa makarantu mallakar jihohi da za su samu lamunin karatu

A baya mun kawo labarin cewa an gano bidiyon wata mace 'yar Najeriya ta na tafiya da manyan zakuna guda biyu ba tare da fargaba ba.

An gano matashiyar ne a cikin bidiyon da ta wallafa ta na tafiya rike da zakunan a wani yanayi na naishadi a wani gidan shakatawa da ke Afrika ta Kudu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.