Har yanzu ba a kama Zakin da ya tsere daga gidan adana namun daji a Kano ba

Har yanzu ba a kama Zakin da ya tsere daga gidan adana namun daji a Kano ba

Sabanin rahotanni daga wasu kafofin watsa labarai na kasar nan suka yada dangane da cewa an samu nasarar cafke zakin da ya tsere daga gidan adana namun daji na jihar Kano, mahukuntan gidan sun yi karin haske.

Mahukanta a gidan adana namun dajin Kano sun ce ya zuwa yanzu ba a kai ga kama zakin da ya kufce ba daga wurin da aka killace shi.

Da yake ganawa da manema labarai na jaridar Kano Focus dangane da tserewar zakin, shugaban gidan adana namun dajin, Alhaji Saidu Gwadabe, ya ce tuni aka baza kwararru a fannin kama zakuna domin lalubo inda ya buya tare da mayar da shi wurin killatarsa.

A cewar Gwadabe, ko kadan batun da wasu kafofin watsa labarai suka yada dangane da kama zakin ba gaskiya bane, domin kuwa ya zuwa yanzu harbin da aka yi wa Zakin har sau biyu da harsashi mai sanya bacci bai yi tasiri ba inda ko gizau bai yi ba, sai dai ya nemi al’umma da su kwantar da hankulansu.

KARANTA KUMA: Ambaliyar ruwa ta hallaka mutane 57 a Jamhuriyyar Nijar

Dangane da irin ta'asar da Zakin ya tafka bayan kufcewarsa, ya yi wa akuyoyi jina-jina biyon bayan afkawa garkensu da ya yi wanda harabar ma'adanar namun dajin. Sai kuma jimina guda a wadda har yanzu an turke shi a kejinta.

Ko a shekarun baya dai gidan adana namun dajin na jihar Kano ya fuskanci tserewar Kadaji wanda lamarin makamancin wannan ya haddasa tsoro a zukatan al'umma musamman wadanda ke makotaka da gidan adana namun dawan.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng