Hadimi Ya Lissafo Ayyuka 72 da Gwamna Dikko Radda Yayi a Katsina Cikin Shekara 1

Hadimi Ya Lissafo Ayyuka 72 da Gwamna Dikko Radda Yayi a Katsina Cikin Shekara 1

  • Hadimin gwamnan na jihar Katsina ya tallata mai girma Dikko Umar Radda da irin ayyukan da yake yi wa jama'a
  • Isah Miqdad ya ce gwamnan ya yi ayyukan ne a cikin shekararsa daya da shiga ofis daga Mayun 2023 zuwa yau
  • Malam Miqdad ya jero ayyukan ne da wasu suka nemi su nuna ana zuzuta gwamnan ne alhali bai tabuka komai ba

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Katsina - Isah Miqdad shi ne babban mai taimakawa gwamnan Katsina a wajen harkokin sadarwa na zamani tun a Yunin 2023.

Isah Miqdad ya jero wasu daga cikin ayyukan Mai girma Dikko Umaru Radda domin maida martani ga masu sukar gwamnatinsu.

Gwamna Dikko Radda
Mai taimakawa Dikko Radda ya lissafo ayyukansa a jihar Katsina Hoto: @Miqdad_Jnr
Asali: Twitter

Hadimin Radda ya tallata Gwamnan Katsina

Kara karanta wannan

Dambarwar Sultan: Dalilai da ka iya jawo Gwamna Aliyu rasa kujerarsa a 2027

Isah Miqdad ya lissafo ayyukan gwamnan ne a shafin X saboda jin abokan adawar siyasa su na cewa ba ya aiki a jihar Katsina.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwanaki aka ji wasu su na ikirarin ana zuzuta abubuwan da Dikko Umaru Radda yake yi, su na zargin ba a ganin komai a zahiri.

A ranar Lahadi, Miqdad ya rufe masu baki da jeringiyar ayyukan da gwamnatin Radda ta gudanar a duka mazabun jihar Katsina.

Ayyukan Gwamnan Katsina, Dikko Radda

Daga cikin ayyukan gwamnatin APC a Katsina akwai gina asibitin wankin koda da daukar mutane 7, 325 aikin S-Power lokaci guda.

Gwamnan ya kirkiro jami’an tsaron sa-kai kuma an tanadan masu kaya da abubuwan hawa tare da gyara makarantun firamare 150.

Ana gina titin Dutsinma zuwa Yandaki da fadada ttitin Kofar Sauri, sannan ana gyaran babban asibitin Faskari bayan gyara na Kafur.

Kara karanta wannan

Abba zai kammala muhimman ayyukan da Kwankwaso ya fara, Ganduje ya yi biris da su

Gwamna Dikko Radda a bangaren ilmi

Gwamnatin Radda ta tura dalibai 42 zuwa Masar domin zama likitoci kuma an rabawa daliban ilmin shari’a da likitanci alawus.

Miqdad ya ce Radda ya karasa wasu ayyukan Aminu Masari kuma ana gina makarantu a garuruwan Charanchi, Musawa da Daura.

Har ila yau gwamnatin ta na gyara sha’anin ruwa, ta habaka kudin shiga kuma ana biyawa dalibai kudin WAEC, NECO da sauransu.

Sai ya rufe jawabinsa da cewa Radda yana cikin gwamnonin da suka fi aiki a Najeriya.

Tinubu ya ba Gwamna Radda mukami

Kwanaki rahoto ya zo cewa Bola Ahmed Tinubu ya ba Gwamna Dikko Umar Radda mukami a kamfanin NDPHC na wutar lantarki.

Shugaban kasa ya dauko gwamnan jihar Katsina ya shiga majalisar gudanar da harkokin wuta tare da gwamnonin Imo, Borno da sauransu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng